in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump: Amurka zata janye jiki daga IRBM
2018-10-21 16:55:02 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana a jiya Asabar cewa, kasarsa zata janye jiki daga yarjejeniyar IRBM, ya kuma yi zargin cewa, kasar Rasha ta dade da sabawa yarjejeniyar.

Trump ya bayyana haka ne a yayin zantawarsa da manema labaru bayan halartar taron gangami a jihar Nevada, inda ya ce, babu yadda za mu yi sai mu cigaba da kera irin wadannan makamai wanda yarjejeniyar ta haramta kerasu.

Mai taimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa John Bolton ya tashi a wannan rana don kai ziyara a kasashe hudu, ciki har da Rasha. Kafofin watsa labarun Amurka sun ruwaito maganar wani jami'in fadar White Housa na cewa, babban burin ziyarar Bolton shine, don sanar da kasar Rasha cewa, kasar Amurka zata janye jiki daga yarjejeniyar.

Yarjejeniyar IRBM ita ce yarjejeniyar kawar da makamai masu linzami na matsakaici da gajeran zango a tsakanin Soviet da Amurka, wadda kasashen biyu suka sa hannu a kai tun a ranar 8 ga watan Disambar shekarar 1987. Bisa yarjejeniyar, kasashen biyu ba zasu cigada da kerawa ko kuma yin gwajin makamai masu linzami dake cin zango tsakanin kilomita 500 zuwa 5500 ba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China