in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Yanayin Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Ciki
2018-10-20 20:32:25 cri
Liu He, mataimakin firaministan kasar Sin, ya halarci wani taron manema labaru a ranar Jumma'a 19 ga wata, inda ya yi bayani kan yanayin da ake ciki a kasar Sin, a fannonin kasuwar hannayen jari, da kamfanoni masu zaman kansu, da hada-hadar kudi, da dai makamantansu. Maganar da Liu He ya yi ta kunshi bayanai masu muhimmanci guda 3.

Na farko: "Kasar Sin ta fara zama kasuwa mafi samar da riba ga jarin da aka zuba"

A cewar Liu He, farashin hannayen jari a kasuwar kasar Sin ya sauka a kwanakin nan, sa'an nan dalilan da suka sa haka na da yawa, wadanda suka hada da matakin kara samar da kudin ruwa a babban bankin kasar, da sauyawar fasalin tattalin arzikin kasar, da dai sauransu. Ya kara da cewa, "Takaddamar ciniki da aka samu tsakanin Sin da Amurka ita ma ta yi tasiri kan yanayin kasuwa, amma hakika wannan tasiri ya fi shafar tunanin mutane, sa'an nan kasashen Sin da Amurka suna shawarwari don daidaita wannan matsala."

Bisa matsayinsa na mai jagorantar aikin shawarwari tsakanin Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki, Liu He ya ce "Sin da Amurka suna shawarwari da juna" ne don nuna cewa, dukkan kasashen 2 ba su son samun takaddamar ciniki, balle tsanantar yanayin. Dangane da wannan batu, za a iya tunawa da maganar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada yayin da yake hira da wakilin kamfanin watsa labaru na CBS a kwanakin baya, inda ya bayyana takaddamar da ake yi tsakanin Sin da Amurka a fannin ciniki a matsayin wani "karamin rikici" maimakon kalmar "yaki" da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka taba amfani da ita. Wannan irin sauyi shi ma zai taimakawa karfafa zukatan jama'ar duniya masu sayen hannayen jari.

Ban da haka, Liu He ya ambaci sakamakon nazarin da wasu kamfanonin zuba jari suka yi, don bayyana yanayin da kasar Sin ke ciki, na "fara zama kasuwar da ta fi samar da riba ga masu zuba jari", gami da yadda kasuwar hannayen jarin kasar ke kara samun daidaituwa. Maganar da za ta kwantar da hankalin masu sayen hannayen jari, da wadanda ke zuba jari na kasar Sin.

Liu ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci kan raya kasuwar hannayen jari, haka kuma ta lura da yadda ake bukatar samun sauyin tsare-tsare ga kasuwar. Saboda haka, gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakai domin samar da wani yanayi na karko a kasuwannin kasar, gami da kwaskwarima ga tsare-tsaren kasuwa. Sai dai Liu ya kara da cewa, ana bukatar gudanar da wadannan manufofi yadda ya kamata.

Na biyu, ya kamata a ba da taimako wajen raya kamfanoni mazu zaman kansu.

Liu He ya taba kiran taron musamman domin yin nazari kan yadda za a ba da taimako ga kanana da matsakaitan kamfanoni masu zaman kansu wajen neman jari, inda ya kuma saurari shawarar wakilan kanana da matsakaitan kamfanoni. Yayin ganawarsa da 'yan jarida, Liu He ya bayyana cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka wajen ci gaba da raya kamfanonin dake karkashin jagorancin gwamnatin kasa, tare da dukufa wajen mara baya ga kamfanoni masu zama kansu. Dangane da wannan batu, ya ba da misalin samar da rancen kudi, inda ya ce, wasu hukumomin suna ganin cewa, ana fuskantar kalubale wajen samar da rancen kudi ga kamfanoni masu zaman kansu, amma ba sa damuwa ko kadan wajen samar da rancen kudi ga kamfanonin mallakar gwamnatin kasa. Dangane da wannan lamari, ya ce, duk wanda ya yi tsammanin haka, yana fuskantar babbar matsala, sabo da idan babu bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu, ba za a tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasa cikin madaidaicin yanayi ba. Kana, in babu ingantaccen tsarin bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu, ba za a iya tsara tsarin masana'antu na zamanin ba. A hakika dai, taimakawa kamfanoni masu zaman kansu, na nufin taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin kasa baki daya.

Haka kuma, ya kamata mu tsaya tsayin daka kan harkoki guda hudu domin raya kamfanoni masu zaman kansu, watau kare tsarin tattalin arziki daga tushe, mai da hankali kan kalubalen dake gaban kanana da matsakaitan kamfanoni masu zaman kansu, ci gaba da yin nazari kan manufofin da za su ba da taimako ga kamfanoni masu zaman kansu wajen neman bunkasuwa, da kuma karfafa kwarewar kamfanoni masu zaman kansu wajen neman ci gaba.

Wannan bayanin da Mr. Liu ya yi, ya nuna babbar gudummawa da kamfanoni masu zaman kansu suka bayar wajen samar da haraji na 50%, da tabbatar da karuwar GDP da 60%, da sabunta fasahohi da 70%, da samar da guraben aikin yi a birane da garuruwa da 80% da kuma karuwar kamfanoni da 90% a kasar Sin, ban da haka kuma, ya nuna kyakkyawan fatan da gwamnatin kasar Sin ke yi wa kamfanonin wajen raya tattalin arzikin kasa da kuma kyautata tsarin tattalin arziki na zamani.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu, da kuma ci gaban shugabannin kamfanonin ba batu ne na tattalin arziki kadai ba, domin sun kasance muhimmin batutuwan siyasar kasa. A nan gaba, za a warware matsalar kamfanonin wajen samun rancen kudi. A sa'I daya kuma, shugaba Xi ya bukaci hukumomin da ba sa son ba da rancen kudi ga kamfanoni masu zaman kansu da su sake tunani.

Bugu da kari, Li He ya yi bayani kan huldar taimakawa juna dake tsakanin kamfanonin dake karkashin jagorancin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, yana mai cewa, a nan gaba, wadannan kamfanoni za su ci gaba da nuna goyon baya ga juna da kuma taimaka juna, ta yadda za su sami ci gaba mai inganci.

Na uku, tarihi ya nuna mana cewa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin na fuskantar makoma mai haske.

Yayin da yake sharhi kan yanayin tattalin arziki da sauye-sauyen tsarin masana'antu a halin yanzu, Liu He ya yi nazari daga wasu muhimman bangarori, ciki har da muhimmin mizanin tattalin arziki, ra'ayoyin kasashen duniya da harkokin hada-hadar kudi. Alal misali, a bangaren hada-hadar kudi, kasar Sin na aiwatar da manufar kudi ta hanyar da ta dace, kuma tsarin hada-hadar kudi da tattalin arziki ya samu ingantuwa sosai, kana, cibiyoyin kudi na gudanar da ayyukan zuba jari tare da yin tunani mai zurfi. Liu He na ganin cewa, ya kamata a maida hankali kan wasu haddura gami da matsalolin da suke wakana sakamakon dalilan tarihi, inda ya jaddada cewa, ya zama dole kasar Sin ta daidaita dangantakar dake tsakanin neman bunkasuwa, da kyautata tsare-tsare, da kuma yin rigakafin haddura, da kuma aiwatar da manufar kudi dake maida hankali kan yin kwaskwarima ga bangaren samar da kayayyaki. Liu He ya kuma bayyana cewa, ya kamata a gaggauta gudanar da wasu muhimman ayyuka guda uku, ciki har da goyon-bayan bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu, da zurfafa yin gyare-gyare ga kamfanonin mallakar gwamnati, tare kuma da inganta kwarewar cibiyoyin kudade don su samar da kyawawan hidimomi ga kamfanoni da daidaikun mutane, da yin kokarin biyan bukatu daga wasu manyan fannoni hudu, ciki har da mutanen dake da matsakaicin kudin shiga, da tsoffin mutane, da sabbin sauye-sauyen kimiyya da fasaha da masana'antu, da kuma neman bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba.

Jiya Jumma'a, kasar Sin ta fitar da alkaluman tattalin arzikin kasar na watan Janairu zuwa Satumbar bana, inda aka nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kashi 6.7 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, kana, tattalin arzikin kasar ya bunkasa ta hanyar da ta dace, kuma ya na da kyakkyawar makoma. A daidai wannan muhimmin lokaci, ana gaggauta sake tsara fasalin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kuma tattalin arzikin kasar Sin na samun ci gaba mai inganci. Mataimakin firaministan kasar Liu He ya zanta da 'yan jaridu, da amsa tambayoyi game da batutuwan da suke jan hankalin mutanen gida da na waje, al'amarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana da kwarewa da karfi wajen raya tattalin arzikinta mai inganci kuma ta hanyar da ta dace.

Duk da cewa ana kara samun abubuwan rashin tabbas a duniya, ya kamata jama'ar kasar Sin su maida hankali kan yin ayyukansu yadda ya kamata, ta yadda za'a shawo kan illolin da abubuwan rashin tabbas ka iya haifarwa. Kamar yadda Liu He ya ce, wahalhalu gami da matsalolin da ake gamuwa da su, wahalhalu da matsaloli ne da suka samo asali yayin da ake neman samun bunkasuwa. Shi ya sa muddin kowa ya fahimci hakan, da kwantar da hankalinsa baki daya, kasar Sin za ta samu kyakkyawar makoma a nan gaba. (Masu fassarawa: Bello Wang, Maryam Yang, Murtala Zhang, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China