in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da mutuwar mutane 55 sanadiyyar rikicin da ya barke a arewacin Nijeriya
2018-10-20 20:03:35 cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya, ta tabbatar da mutuwar mutane 55, sanadiyyar wani rikicin kabilanci da ya barke ranar Alhamis, a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Yakubu Sabo Abubakar ne ya tabbatar da adadin ga kamfanin dillanci labarai na Xinhua, inda ya ce rikicin ya barke ne tsakanin matasan kabilar Hausa da ta Adara.

Rahotanni sun ce lamarin ya auku ne sanadiyyar sabanin da aka samu kan inda 'yan kasuwa za su rika sauke kayayyakinsu na sayarwa ranar Alhamis da ake cin kasuwa a kauyen Kasuwa Magani, wanda ke da nisan kilomita 31 daga birnin jihar.

Yakubu Abubakar ya kara da cewa 'yan sanda sun cafke mutane 22 dake da alaka da tashin rikicin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China