Binciken farko da ofishin mai shigar da kara na kasar ya gabatar, ya bayyana cewa, fada ta kaure tsakanin Jamal Khashoggi da wadanda ya hadu da su a ofishin jakadancin Saudiyya dake Instanbul, al'amarin da ya kai ga mutuwarsa.
Ofishin ya kuma tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da bincike game da lamarin, yana mai cewa za a hukunta dukkan wadanda ke da hannu.
A baya dai, Saudiyya ta sha musanta zargin da ake wa masarautar kasar na kashewa ko tsare Khashoggi. (Fa'iza Mustapha)