in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin suna da makoma mai haske
2018-10-18 20:17:34 cri

A kasar Sin, gwamnati na daukar manufar "raya kamfanoni masu zaman kansu, da taimakawa mutane masu kamfanonin lami lafiya" (ko kuma "Lami Lafiya Guda 2" a takaice). Kwanakin baya, an gudanar da jerin tarukan yayata manufar "Lami Lafiya Guda 2" a birnin Wenzhou dake lardin Zhejiang na kasar Sin. Da ma a wannan birni ne aka fara raya tattalin arzikin sassa masu zaman kansu na kasar Sin, kuma yanzu ya zama inda aka fara aiwatar da manufar "Lami Lafiya Guda 2". Ma iya cewa, birnin ya sake daukar nauyin kasancewa mai jagorantar aikin gyare-gyare da bude kofa na kasar Sin.

An gabatar da manufar "Lami Lafiya Guda 2" a wajen taron karo na 19 na wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ya gudana shekara daya da ta wuce, tare da nufin "kafa sabuwar hulda tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa, da raya kamfanoni masu zaman kansu, da taimakawa mutane masu kamfanonin lami lafiya".

Hakika cikin shekaru 40 da suka wuce, kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin sun yi amfani da albarkatu kimanin kashi 40% na kasar Sin, wajen samar da GDP da ya kai kashi 60% na kasar, da mika harajin da ya kai kashi 50%, da samar da sabbin fasahohi, da kayayyaki da suka kai fiye da kashi 70%, da guraben aikin yi da suka kai fiye da kashi 80% na kasar. Inda har ma aka tabbatar da wani ra'ayi na masu kamfanoni na kasar Sin, na neman samar da sabbin fasahohi, da aminci, da kishin kasa, da kuma matukar son aikin da suke yi.

Yanzu haka a lokacin da kasar Sin ke kokarin sauya fasalin tattalin arzikinta zuwa wanda ke da cikakken inganci, musamman ma ta la'akari da yanayin da ake ciki na fama da takaddamar ciniki a duniya, kamfanoni masu zaman kansu, wadanda suke samar da kashi 45% na kayayyakin da ake fitarwa daga kasar Sin, sun fi fuskantar matsin lamba. Saboda haka suna bukatar kara kokari a fannonin kirkiro sabbin kayayyaki, da kula da kamfani, da neman rance da jari, da rage yiwuwar samun hadari, da dai sauransu. Ban da haka kuma, suna bukatar samun tallafi daga gwamnati.

A nasa bangare, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taba jaddada cewa, manufar "Lami Lafiya Guda 2" ta shafi tattalin arziki, gami da siyasa. A kwanakin baya, ya yi rangadi a lardin Liaoning dake arewacin kasar Sin, inda ya bukaci a samar da muhalli mai kyau ga kamfanoni masu zaman kansu, a fannonin shari'a, gami da harkokinsu na yau da kullum. Wannan ra'ayin da ya bayyana, ko shakka babu, zai karfafawa masu kamfanonin gwiwarsu.

Wata fasaha mai kyau da Sinawa suka koya, bayan aka fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da kuma bude kofa ga waje ita ce, "mu gwada da farko". Cikin shekaru 40 da suka gabata, mutanen birnin Wenzhou sun cimma nasarori da dama a fannin raya kamfanoni masu zaman kansu, har sun fitar da "fasahohin Wenzhou", suka kuma fara yin suna a fadin kasar Sin, domin kokarinsu wajen kafa sabbin kamfanoni. A halin yanzu, a duk mutum daya cikin mutane 10 na birinin Wenzhou na mallakar kamfani, ta yadda har adadin kamfanoni masu zaman kansu ya kai kashi 99.5 bisa dari a birnin Wenzhou. Shi ya sa, gwamnatin kasar Sin ta mai da birnin Wenzhou wuri na farko da ta aiwatar da manufar "lami lafiya guda biyu", domin sa kaimi ga shugabannin kamfanoni masu zaman kansu da su yada fasahohi, da manufofi, da kuma matakansu wajen gudanar da harkokin kamfanoninsu a duk fadin kasar Sin, ta yadda za a fitar da sabuwar hanyar raya kamfanoni masu zaman kansu a duk fadin kasar Sin.

Don gane haka, gwamnatin birnin Wenzhou ya sanar da cewa, za a dukufa wajen raya harkokin kasuwanci a birnin, don ya kasance kan gaba a duk fadin kasar Sin, har a kai ga kafa wani tsarin raya tattalin arziki da ya dace da halin da kasar Sin ke ciki nan zuwa shekarar 2025. A sa'i daya kuma, za ta gabatar da manyan matakai guda goma, da suka hada da "ba da tallafi yadda ya kamata ga kanana da matsakaitan kamfanoni", da "kafa yanayi mafi kyau na aiwatar da harkokin kasuwanci", da dai sauransu, domin cimma wannan buri.

Kana, wadannan matakai guda goma da birnin zai dauka, suna kunshe da muhimman batutuwa guda uku.

Da farko, kafa sabuwar huldar dake tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. An yi ta jaddada wannan batu a yayin cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 19. Ma'anar sa ita ce, ya kamata gwamnatin wurin ta taimaka wa kamfanoni masu zaman kansu, wajen warware wasu matsalolin da za su gamu da su a yayin da suke neman ci gaba, amma kada gwamnatin wurin ta yi cin hanci da karbar rashawa. A sa'i daya kuma, ya kamata shugabannin kamfanonin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamta, kuma bisa dokokin kasar Sin.

Bisa labarin da aka samu, an ce, gwamnatin birnin Wenzhou za ta fitar da jerin matakai, domin tabbatar da kafa sabuwar hulda a tsakanin 'yan siyasa, da 'yan kasuwa yadda ya kamata, inda za ta yi cikakken bayani kan abubuwan da aka hana a yi, a yayin gudanarwar hadin gwiwa tsakanin 'yan siyasa da 'yan kasuwa, kana a karfafa ayyukan sa ido da dai sauransu, ta yadda za a iya tabbatar da bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu a birnin Wenzhou yadda ya kamata.

Na biyu, ya kamata a kara kyautata muhallin yin cinikayya. Bisa sabuwar manufar da gwamnan babban bankin kasar Sin Yi Gang ya bulo da ita, dukkanin kamfanoni, ko na gwamnati, ko ba na gwamnati ba, za su shiga takara cikin adalci, da samun kariya bisa doka. Birnin Wenzhou zai yi namijin kokarin inganta tsarin samar da hidimomin gwamnati daga dukkan fannoni, da saukakawa mutane da kamfanoni matakan da za su bi wajen tafiyar da harkokin gwamnati, da bada tabbaci ga daidaikun mutane, gami da kamfanoni daban-daban, don su gudanar da sana'o'i da harkokin cinikayya ta hanyar da ta dace, a wani kokari na kirkiro kyakkyawan muhallin yin cinikayya na kasa da kasa.

Na uku, ya kamata a tallata kyawawan halayen shugabannin kamfanonin kasar Sin. Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, shugabannin kamfanoni muhimman mutane ne wadanda ke kokarin habaka harkokin tattalin arziki, kana, irin kyawawan dabi'u gami da halayensu na samar da babban karfi ga bunkasuwar kamfanoni. Yayin da yake kokarin aiwatar da manufar "lami lafiya guda biyu", birnin Wenzhou zai ci gaba da kyautata tsarin tantance imanin kamfanoni daban-daban, da kafa tsari na dogon lokaci, wanda zai bada kariya ga duk wani nau'in kamfani, ciki har da na gwamnati da masu zaman kansa, tare kuma da kokarin yayata kyawawan dabi'u da halayen shugabannin kamfanoni daban-daban. Muna iya ganin cewa, shugabannin kamfanoni a birnin Wenzhou, za su kara nuna karfin yin kirkire-kirkire, da na takara a lokacin da ake kawo sauye-sauye ga tattalin arzikin kasar Sin.

A matsayin birni na farko da za'a fara aiwatar da manufar "lami lafiya guda biyu", Wenzhou za ta zama abar misali, wadda za ta bude wata sabuwar hanya ga bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu, da harkokin samar da hidimomin gwamnati, har ma za ta taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin duk kasar Sin cikin dogon lokaci. (Masu fassarawa : Bello Wang, Maryam Yang, Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China