Wasu manyan jami'ai biyu na fadar White House sun bayyana haka ne a yayin wani taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, inda suka ce, manufar "terminal dues" da kawancen ke bi a halin yanzu, wani nau'in rashin adalci ne ga kasar Amurka, kasashe da dama suna amfani da Amurka don biyan bukatunsu wajen biya kudin hidima tsakanin kasa da kasa.
A waje guda kuma, sanarwar ta ce, ko za a cimma sabuwar yarjejeniyar ko a'a, kasar Amurka zata bi tsarin "terminal dues" da ta tsarawa kanta kafin ranar 1 ga watam Janairun shekarar 2020. (Bilkisu)