in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Standard Chartered: kudin RMB na kasar Sin na da kyakkyawar makoma a Afirka
2018-10-18 11:54:45 cri

A yayin da ake hanzarta bunkasa cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, yawan masana'antu da kamfanoni na kasar Sin wadanda suke shiga kasashen Afirka yana karuwa. Sakamakon haka, wasu bankunan kasa da kasa sun kyautata zaton makomar kudin RMB na kasar Sin a Afirka. A kwanan baya, wasu jami'an bankin Standard Chartered sun bayyanawa wakiliyarmu dake Nairobi, hedkwatar kasar Kenya cewa, suna cike da imani ga matakin yin amfani da kudin RMB a kasuwannin kasashen Afirka. Bugu da kari, yanzu wasu kasashen yammacin duniya sun zargi kasar Sin cewa rancen kudin da kasar Sin ke samarwa kasashen Afirka sun zama "tarkon cin bashi", game da wannan batu, jami'ar bankin Standard Chartered tana ganin cewa, rancen kudin da kasar Sin take samarwa kasashen Afirka wajen samar da kayayyakin more rayuwar jama'a zai shafe dogon lokaci mai zuwa, irin wadannan kayayyaki za su kawowa al'ummomin sauye-sauye da kuma moriyar a zo a gani.

Madam Jean Lu, mataimakiyar gwamnan reshen kasar Sin na bankin Standard Chartered ta bayyana cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" wata babbar manufa ce da shugaban kasar Sin ya gabatarwa duk duniya, bisa wannan shawara, a cikin shekaru 5 da suka gabata, an tsara shirye-shiryen samar da ayyuka fiye da 2700, wadanda za su haifar da kudin cinikayya dalar Amurka biliyan dubu 5 a wasu kasashen duniya. A matsayin wadda take aiki a wani bankin kasa da kasa, tana ganin cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" na kawowa zaman al'ummomin kasashen Afirka sauye-sauye da sakamako na zo a gani. Jean Lu ta ce, "Zan iya gaya muku wasu alkaluman da suke burge ni. A cikin shekaru 5 da suka gabata, kasar Sin ta kafa yankunan cinikin hadin gwiwar bunkasa tattalin arziki da cinikayya 113 a kasashe 46, inda ta zuba jari dalar Amurka biliyan 35, sannan yawan kamfanonin da suka kafa rassansu a ciki ya kai fiye da 4500. Bugu da kari, wadannan yankunan ciniki sun samar da haraji dalar Amurka biliyan 3 tare da guraben aikin yi dubu 287. Wadannan alkaluman da aka samu ne sakamakon aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya', al'ummomin wurin suna kuma cin gajiyarsu."

A 'yan watannin da suka gabata, an sha sauraran wasu shakkun da aka nunawa shawarar "ziri daya da hanya daya", wai ana cewa, shawarar ta sa wasu kasashe cin basussuka masu tarin yawa. Madam Carmen Ling, wadda take kula da harkokin reshen Hongkong na bankin Standard Chartered dake shafar shawarar "ziri daya da hanya daya" ta bayyana cewa, ta san wadannan zarge-zarge. Amma a ganinta, ayyukan samar da kayayyakin more rayuwar al'umma za su shafi wani dogon lokaci. Ko da yake an riga an shafe shekaru 5 ana kaddamar da shawarar "ziri daya da hanya daya", amma har yanzu ana cikin farkon lokaci ne. Madam Carmen Ling tana mai cewa, "A ganina, aikin samar da kayayyakin more rayuwar al'umma zai shafi wani dogon lokaci. Shi ne kuma dalilin da ya sa wasu masu zuba jari ba su son samar da irin wadannan rancen kudi. A 'yan shekarun baya, kasar Sin ta samar da dimbin rancen kudi ga wasu kayayyakin more rayuwar al'umma. Tabbas ne yawan basusukan da wasu kasashe suka ci zai karu, amma za su iya mayar da su cikin dogon lokaci mai zuwa, a cikin wannan dogon lokaci, tattaliln arziki da al'ummomin wadannan kasashe za su ci gajiyar a zo a gani daga wadannan kayayyakin more rayuwar al'umma."

Yanzu dimbin 'yan kasuwa na kasar Sin suna neman izinin kasuwanci a Afirka, wato ta kasance tamkar wata kasuwa wadda ke samun bunkasuwa mafi sauri a duk fadin duniya. Kasashen Afirka ma suna kokarin fitar da karin kayayyaki ga kasuwannin kasar Sin. Amma har yanzu ana amfani da dalar Amurka kawai a lokacin da suke yin ciniki. Madam Carmen Ling tana ganin cewa, "Koda yake yawan kudin cinikayya da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen da shawarar 'ziri daya da hanya daya' ke shafar ya yi yawa sosai, amma a hakika dai, idan mun kwatanta kasuwar yin amfani da dalar Amurka, za mu iya ganin cewa, kasuwar yin amfani da kudin RMB tana matakin farkon neman ci gaba. Sabo da haka, idan ana yin ciniki a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, an fi son yin amfani da kudin RMB na kasar Sin kai tsaye. Shi ne dalilin da ya sa bankin Standard Chartered yake son gwada yin haka." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China