in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba ta jin tsoron yakin cinikayya ba saboda ci gaban tattalin arzikin da ta samu
2018-10-17 10:59:36 cri

Yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke zantawa da jagoran shirin kamfanin CBS Lesley Stahl, a daren ranar 14 ga wannan wata, agogon gabashin kasar, ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ta kasa daukar karin matakan mayar da martani ga kasarsa, yayin da sassan biyu ke yakin cinikayya, inda ya kara da cewa, matsalar da Sin da Amurka suke fuskantar ba yakin cinikayya ba ce, karamar rigima ce wadda babu tsanani ko kadan.

Yayin da yake zantawa da jagoran shirin kamfanin CBS, Trump ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasa daukar karin matakan mayar da martani ga kasarsa bisa dalilin cewa, kwanan baya Amurka ta kara karbar harajin kwastan kan kayayyakin kasar Sin da ke shiga kasarsa, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 100, amma kasar Sin ta mayar da martanin kara karbar harajin kwastan kan kayayyakin Amurka dake shigowa kasar, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 53 da miliyan 100 kawai, a don haka, ya dauka cewa, zai yi wuya kasar Sin ta ci gaba da mayar da martani ga kasarsa.

Amma hakika yakin cinikayya ba shi da nasaba da adadin kudin wato yakin cinikayya ba wasan lamba ba ne, sai dai yana shafar moriyar kamfanoni da masu sayayya da yawan gaske. Gwamnatin Amurka ta kasa kula da adawar da ake nuna mata, ta ci gaba da habaka yakin cinikayya, kuma dalilinta shi ne, kokarin kiyaye matsayinta na farko a duniya, amma ba zai yiyu gwamnatin kasar Sin ta yi haka ba, saboda tana da hankali, tana ba da muhimmanci matuka kan moriyar al'ummumomin kasashen duniya, a don haka take kokarin kiyaye tsarin cinikayya maras shinge dake tsakanin bangarori da dama. A karkashin irin wannan yanayi, kasar Sin ta dauki matakin da ya fi dacewa bisa tushen yin hakuri, makasudinta shi ne, hana bazuwar yakin cinikayya ta hanyar mayar da martani mai karfi.

Hakika hakurin da kasar Sin ta nuna bai nuna cewa, ta kasa daukar karin makatan mayar da martani ba, akasin haka, kasar Sin tana da babbar kasuwa, tattalin arzikinta shi ma ya samu ci gaba cikin sauri, ko shakka babu kasar Sin ba ta ji tsoron yakin ciniyayya ba ko kadan.

Da farko, tattalin arzikin kasar Sin yana gudana lami lafiya, har karuwarsa ya kai kaso 6.7 zuwa 6.9 bisa dari a cikin shakaru 3 da suka gabata, kana karuwarsa na dogara ne kan sayayya da hidima da kuma bukatun cikin gida, a maimakon dogaro kan fitar da kayayyaki zuwa ketare da samun jarin waje a baya. Ban da haka, kasar Sin tana da cikakken tsarin masana'antunta, haka kuma tana da babbar kasuwar sayayya wadda ke da karfi a asirce, duk wadannan suna ba da tabbaci ga kasar da ta dakile matsalar da yakin cinikayyar ke kawowa. A shekarar 2017, adadin GDP na kasar ya kai dala biliyan dubu 12 da 700, adadin kudin da ta samu daga fitar da kayayyaki zuwa ketare ya kai dala biliyan 2260, shi ya sa matakin kara karbar harajin kwastan da Amurka ta dauka kanta ba zai yi tasiri ba. Kwanan baya bankin duniya ya taba fitar da wani gajeren rohoton tattalin arzikin kasar Sin, inda ya bayyana cewa, har yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana samun bunkasuwa cikin sauri.

Na biyu, kasar Sin tana kara bude kofa ga ketare, lamarin da ya taimakawa kasar yayin da take mayar da martani. Tun farkon bana, kasar Sin ta fara aiwatar da wasu sabbin manufofin bude kofa ga ketare, hakan ya sa kasar ta kara shigo da jarin da 'yan kasuwan kasashen ketare suka zuba. Misali kamfanin BMW na Jamus ya kara zuba jarin da yawansa ya kai kudin Euro biliyan 3 a kasar Sin, kamfanin Exxon Mobil na Amurka ya riga ya daddale yarjejeniyar zuba jarin dala biliyan 10 a kasar Sin, kamfanin Tesla na Amurka zai kafa reshensa na farko a kasar waje a birnin Shanghai na kasar Sin. Hakazalika, kasar Sin ta sanar da cewa, tun daga ranar 1 ga watan Nuwamban bana, za ta rage haraji kan kayayyakin da yawansu ya kai 1585, da haka, matsayin harajin kwastan zai ragu daga kaso 9.8 bisa dari na bara zuwa kaso 7.5 bisa dari.

To, abin bakin ciki shi ne an lura cewa, Amurka tana fama da matsala, bisa alkaluman da aka samu, an ce, gibin cinikayyar Amurka a kasar Sin a watan Satumba ya sake kai wa matsayin koli a tarihi har ya kai dala biliyan 34 da miliyan 100, adadin da ya karu da kaso 13 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin a shekarar 2017, a don haka tashar yanar gizo ta VOX ta Amurka ta yi sharhin cewa, manufar da gwamnatin Trump ke aiwatarwa kan yakin cinikayya ba ta da amfani ko kadan.

A takaice dai, ana iya cewa, ba wanda zai samu moriya daga yakin cinikayya, a don haka kasar Sin ta bayyana sau tari cewa, ba ta son yin yakin cinikayya da Amurka ko sauran abokan cinikayya, amma ba ta jin tsoron yakin saboda ci gaban tattalin arzikin da ta samu. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China