in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai dace a goyi bayan tsara manufofin hana bunkasuwar Sin ta hanyar yin amfani da batun karamar na'urar lantarki ba
2018-10-17 10:47:42 cri
Mujallar Bloomberg Businessweek ta kasar Amurka ta ruwaito a kwanakin baya cewa, kasar Sin ta sanya wata karamar na'urar lantarki cikin kayayyakin da kamfanonin Amurka kimanin 30 suka kera, domin neman bayanan sirri. Amma kamfanonin da abin shafa kamar su Apple Computer Inc. da Amazon.com Inc. da Super Micro sun bayar da sanarwoyi, inda suka musunta labarin tare da bayyana shi a matsayin maras tushe. Hukumar tsaron kasar Amurka ta kuma furta cewa, babu dalilin shakku kan sanarwoyin da kamfanonin Amurka suka bayar kan labarin da Bloomberg Businessweek ta bayar.

Mashahurin masanin nazarin lamuran duniya na kasar Amurka Doctor Robert Kuhn, ya bayyana cikin wani shirin telebijin na mujallar Bloomberg cewa, kila za a iya samun wasu bayanan sirri kadan ta hanyar sanya karamar na'urar lantarki a cikin kamfutan wasu kamfanonin Amurka, amma idan aka gano batun, za a lalata dukkan cinikin samar da kayayyaki zuwa wannan kasa. Babu shakka, babu wanda yake son tsara wannan kuduri mai illa.

A ganin Kuhn, batun sanya karamar na'urar lantarki cikin kwamfuta ba batu mai tsanani ba ne, amma wasu suna son yin amfani da wannan batu don nuna goyon baya ga tsara sabbin manufofin hana bunkasuwar Sin, lallai wannan abu ne da bai dace ba sam. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China