in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi tir da kisan jami'ar Red Cross a Nijeriya
2018-10-17 10:45:42 cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da kisan jami'ar bada agaji ta kungiyar Red Cross, a arewa maso gabashin Nijeriya.

Wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, ta ce Antonio Guterres ya bayyana damuwa game da tsaro da lafiyar sauran wadanda aka yi garkuwa da su, yana mai kira da a yi gaggawar sako su.

Sakatare Janar din ya jaddada cewa, dole ne dukkan bangarorin dake rikici su kare jami'an agaji dake aikin ceton rayukan miliyoyin jama'a dake cikin bukata a arewa maso gabashin Nijeriya.

Masu kaifin kishin addini da suka sace Jami'ar mai suna Hauwa Liman ne suka kashe ta a jiya Litinin, bayan wa'adin da suka dibarwa gwamnati ya kare. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China