in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Sake nazari kan sharhin Thomas Friedman
2018-10-16 19:37:24 cri

Mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence, ya yi wani jawabi a kwanakin baya, inda ya yi suka kan manufofin cikin gida da na diplomasiyya na kasar Sin ba tare da hujja ko dalili ba. Zancen da mista Mike Pence ya yi, ya sa an tuna da wani sharhi mai taken "shekaru 7 masu muhimmanci" da marubucin kasar Amurka Thomas Friedman ya rubuta, kuma jaridar New York Times ta wallafa a yau shekaru 10 da suka gabata.

A lokacin, mista Friedman ya zauna wurin da aka gudanar da bikin rufe wasannin Olympics na birnin Beijing, inda ya kalli nune-nunen fasahohin al'adu masu kayatarwa, da masu kunshe da fasahohi na kasar Sin, sa'an nan a sabili da burgewar da ya samu, ya rubuta wannan sharhi.

A cikin sharhinsa, ya lura da cewa, birnin Beijing na kasar Sin ya samu damar karbar bakuncin gasar Olympics karo na 29 a watan Yulin shekarar 2001, yayin da kasar Amurka ta gamu da harin ta'addancin da aka kai mata a ranar 11 ga watan Satumban shekarar. Daga bisani kasashen 2 sun hau hanyoyi masu banbanta.

Thomas Friedman ya bayyana cewa, yayin da suke shirya karbar bakuncin gasar wasannin Olympic, muna kokarin dakile kalubalen kungiyar al-Qaida. Yayin da suke gina filayen wasannin motsa jiki da tasoshin jiragen kasa dake karkashin kasa, da filayen saukar jiragen sama da hanyoyi da filayen wasan kwallo, muna kokarin kera na'urorin tantance hadari, da manyan motoci masu mallakar makamai da jiragen sama maras matuka masu amfanin tantance hadari. Yana ganin cewa, a cikin shekaru bakwai masu zuwa, ya kamata Amurka ta mai da hankali kan aikin gina kasar ta.

Amma abin bakin ciki shi ne a cikin shekaru goma da suka gabata, har kullum Amurka tana kan hanyar lalata moriyar sauran kasashe, a maimakon haka, kasar Sin tana nuna kwazo da himma domin aiwatar da manufar yin kwaskwarima, da bude kofa ga ketare, tare kuma da sanya kokari tare da sauran kasashe domin gina kyakkyawar makomar bil Adama.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, duk da cewa gwamnatin Obama ta sanar da cewa, Amurka ta daina yake-yake a kasashen Afganistan da Iraki, amma ta sake kutsa kai cikin kasar ta Syria, har ta rushe kasar Libya, kana ta tura jiragen ruwan yaki kasar kaso 60 bisa dari zuwa tekun Pasifik, lamarin da ya kawo hadari ga yankin.

Game da Donald Trump da ya ci zaben shugaban kasar Amurka bisa kalmar rantsuwa ta "Sanya Amurka ta sake yin girma", ba ya yi la'akari da makomar bai daya da moriya ta bil'adama, har ya sanya kasarsa ta janye jiki daya bayan daya daga wasu yarjejeniyoyin kasa da kasa da hukumomin MDD, ciki har da yarjejeniyar kasashen yankin Pacific ta cinikayya ko (TPP), da yarjejeniyar sauyin yanayi na Paris, da kungiyar UNESCO, da hukumar kula da hakkin bil Adama ta MDD, da yarjejeniya game da batun nukiliyar Iran a dukkan fannoni da dai sauransu a cikin shekara daya. Ya yi ta maida moriyar kasar Amurka a gaban ka'idodjin kasa da kasa, da alkawuran da kasar ta yi a duniya, hakan ya gamu da adawa da zargi daga kasashe da dama.

Amma, duk da haka Trump ya ci gaba da yin haka. A kwanan baya, a yayin da yake zantawa da manema labaru na gidan talabijin na Fox na kasar Amurka ta wayar tarho, ya yi zargin cewa, Sinawa na dauko dalar Amurka biliyan 500 daga wajen kasar Amurka a kowace shekara, a cewarsa wai kasar Amurka ce ta raya kasar Sin.

Har ma ya yi koke-koken cewa, "Sinawa sun dade suna shan jin dadin zaman rayuwa." Shin Amurka ba ta samu kayayyaki kirar kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 500 a cikin cinikayyar da ke tsakanin kasashen biyu ba? Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Colin Powell ya bayyana cewa, Amurka ta ci gajiya sosai daga bunkasuwar kasar Sin, kuma kayayyaki kirar kasar Sin masu inganci da rahusa, sun biya bukatun jama'ar Amurka sosai. Bugu da kari, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Madam Madeleine Korbel Albright ta nuna cewa, farfadowar kasar Sin sakamako ne na himmatuwar jama'ar Sin. Kana gaza daukar nauyin da ke wuyan Amurka kan lamuran kasashen duniya ya bai wa Sin damar ci gaba.

Ko shakka babu, akwai dalilai da dama da suka sa shugabannin Amurka suka yi korafi kan kasar Sin. Alal misali, kasar Sin ta samu bunkasuwa cikin saurin gaske, idan aka kwatanta da na shekaru goman da suka gabata. A shekara ta 2008, an kaddamar da layin dogo mai saurin tafiya na farko a yankin kasar Sin, wato layin dogon da ya hada biranen Beijing da Tianjin, haka kuma a halin yanzu, ban da jihohin Tibet da Ningxia, an kaddamar da layukan dogo wadanda saurin tafiyarsu ya zarce kilomita dari biyu a kowace sa'a, a dukkanin sauran larduna, da yankuna, gami da manyan biranen kasar Sin. Amma game da muhimman ababen more rayuwar al'umma da darajarsu ta kai dala triliyan 1.5 da Donald Trump ya yi alkawarin ginawa, har yanzu ba'a aiwatar da su ba. Haka kuma, filin saukar jiragen sama na LaGuardia dake birnin New York, wanda Friedman ya yi suka a kan sa shekaru goman da suka gabata, har yanzu bai canja ba, har ma ya kara lalacewa.

A shekarar 2017, adadin mutane masu fama da talauci na kasar Sin ya ragu daga miliyan dari 2 a shekarar 2008 zuwa kimanin miliyan 30, kuma gwamnatin kasar Sin ta sanar da kudurin ta na kawar da kangin talauci gaba daya a kasar nan da shekarar 2020. Amma bisa wani rahoton shekara-shekara da babban bankin Amurka watau FED ya fidda a watan Mayu, an ce, bisa binciken da bankin ya yi wa wasu 'yan Amurka, kimanin kashi 40 bisa dari daga cikinsu ba su iya biyan kudin agajin gaggawa na dallar Amurka dari 4 ba, sai dai su nemi rancen kudi ko sayar da kayayyakinsu.

Neman ci gaba shi ne hanya kadai da ya kamata mu bi. Kada a nuna hassada kan Sinawa don sun ji dadin zaman rayuwarsu, ya kamata a yi koyi daga wajensu, kan yadda suke dukufa wajen gudanar da ayyukansu. Sabo da ya kamata dukkanin al'ummomin Sin da na Amurka su ji dadin zaman rayuwarsu a wannan duniya. (Marubuciya: Lv Xiaohong; Masu Fassarawa: Jamila Zhou, Kande Gao, Bilkisu Xin, Bello Wang, Murtala Zhang, Maryam Yang, dukkansu ma'aikatan CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China