in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya yi shawarwari da takwaransa na Holand
2018-10-16 13:08:05 cri

Jiya da safe, agogon wurin, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Holand Mark Rutte a fadarsa dake birnin Hague na kasar, inda Li ya bayyana cewa, kasarsa tana son yin kokari tare da kasar ta Holand domin kiyaye tsarin cinikayyar kasa da kasa maras shinge dake tsakanin bangarori da dama ta hanyar gudanar da hadin gwiwa ba tare da wata rufa rufa ba.  

Holand kasa ce ta mambar EU wadda ke sahun gaba inda kasar Sin ke zuba jari kai tsaye, kana ta kai matsayi na biyu wadda ke gudanar da cinikayya dake tsakaninta da kasar Sin, haka kuma tana matsayi na uku wadda ke samun jarin waje daga kasar Sin, ziyarar da firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ke yi a kasar, ziyara ce ta farko da ya kai kasar cikin shekaru 14 da suka gabata, yayin shawarwarin da ya yi da takwaransa na Holand Mark Rutte, ya bayyana cewa, "Makasudin ziyararsa a Holand shi ne domin ciyar da huldar dake tsakanin kasashen biyu gaba, kasar Sin tana son kara zuba jari a Holand domin raya aikin gona da aikin samar da hidima na kasar, ana fatan kasashen biyu zasu kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata."

Kan batun game da kwaskwarimar tsarin kungiyar cinikayyar duniya, Li ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana son kara karfafa cudanyar dake tsakaninta da kasar ta Holand kan wannan batu, yana ganin cewa, ya kamata a ci gaba da nacewa ga manufar gudanar da cinikayya maras shinge ba tare da rufa rufa ba yayin da ake yin kwaskwarimar tsarin kungiyar cinikayyar duniya, ta haka za a iya kiyaye hakki da moriyar kasashe masu tasowa, tare kuma da rage ratar dake tsakanin kasashen da suka ci gaba da kasashe masu tasowa, a sa'i daya kuma, za'a nace ga ka'idar yin shawarwarin dake tsakanin kasashe daban daban, bai dace ba a mayar da wasu kasashe saniyar ware a yayin da ake gudanar da cinikayyar kasa da kasa, ta yadda daukacin kasashen duniya zasu cimma burin samun ci gaba tare sannu a hankali, a cewarsa: "Muna son nuna matsayinmu tare da kasar Holand kan manufar kiyaye tsarin cinikayya maras shinge dake tsakanin bangarori da dama, a halin da ake ciki yanzu, yanayin tattalin arziki da siyasar da kasashen duniya ke ciki yana da sarkakiya, haka kuma ana fama da matsalar rashin tabbaci a fannoni daban daban, a don haka ya dace mu yi kokari tare domin kiyaye tsarin cinikayya maras shinge dake tsakanin bangarori da dama."

Firayin minister Li ya jaddada cewa, kamata ya yi sassan biyu wato Sin da Holand su nunawa kasa da kasa matsayin da suka cimma wajen kiyaye tsarin duniya wanda ke karkashin jagorancin ka'idojin da aka tsara, su ma zasu ci gaba da yin kokari tare domin sa kaimi kan cinikayya da zuba jari dake tsakaninsu da kuma tsakanin kasar Sin da kasashe mamboin EU.

Li ya kara da cewa, kasarsa tana goyon bayan yarjejeniyar dakile matsalar sauyin yanayi ta Paris, zata ci gaba da sanya kokari matuka domin cika alkawarin da ta yi kan batun, ya kara da cewa, ya kamata kasashen duniya su sauke nauyin dake bisa wuyansu domin dakile matsalar lami lafiya, tare kuma da mai da hankali kan ci gaban kasashe masu tasowa. Li ya bayyana cewa, "Kasashen biyu wato Sin da Holand suna fuskantar matsala iri guda wato tsoffafi a kasashen suna karuwa cikin sauri, shi ya sa muna fatan zamu kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninmu a wannan fanni, misali bude kasuwar samar da hidima ga tsofaffi, nan gaba bari mu kara tattaunawa kan batun dake tsakaninmu."

A nasa bangare, firayin ministan Holand Mark Tutte ya bayyana cewa, kasarsa tana maida hankali matuka kan huldar dake tsakaninta da kasar Sin, ita ma tana son kara karfafa amincewar juna dake tsakaninta da kasar Sin, haka kuma tana son kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni, musamman ma a fannonin ci gaban tattalin arziki, da zamanintar da garuruwa da birane, da dakile matsalar sauyin yanayi, da aikin kula da tsoffafi, da cudanyar dake tsakaninsu a cikin harkokin MDD da kungiyar G20, tare kuma da kiyaye tsarin gudanar da cinikayya maras shinge tsakanin bangarori da dama.

Bayan shawarwarin, an daddale wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da harkar kudi da makamashi da aikin gona dake tsakanin kasashen biyu a gaban firayin ministocin biyu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China