in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan shugabannin 'yan kasuwan Afrika za su yi taro a Kenya don bunkasa cinikayya a nahiyar
2018-10-16 11:04:58 cri
A mako mai zuwa kasar Kenya za ta karbi bakuncin taron wuni biyu wanda zai tattara shugabannin 'yan kasuwa daga kasashen Afrika, inda zasu tattauna hanyoyin da zasu kyautata bunkasuwar harkokin cinikayya a tsakanin kasashen Afrika.

Majalisar kula da harkokin ciniki da masana'antu ta kasar Kenya ta sanar a jiya Litinin cewa, za'a gudanar da taron ne tsakanin ranakun 23-24 ga watan nan na Oktoba wanda zai mayar da hankali game da hanzarta aiwatar da yarjejeniyar cinikin cikin 'yanci ta kasashen Afrika wato (AfCFTA), da kuma tsare tsaren harkokin kasuwanci a tsakanin al'ummar nahiyar.

Da yake jawabi gabanin gudanar da taron, shugaban majalisar ciniki da masana'antun kasar Kenya Kiprono Kittony, wanda kuma shi ne daya daga cikin mataimakan shugaban wakilan Afrika a majalisar ciniki ta kasa da kasa wato (WCF), ya ce taron ya zo ne a lokacin da ya dace, kuma yana da tasiri wajen warware manyan matsalolin da ke haifar da cikas wajen bunkasuwar harkokin cinikayya a tsakanin kasashen Afrika.

Taron zai samu halartar shugaban majalisar ciniki ta kasa da kasa (WCF) Peter Mihok, da shugabannin majalisar ciniki ta kasashen Afrika 59.

Kiprono ya ce taron zai kara zaburar da shugabannin 'yan kasuwa na Afrika wajen fahimtar irin dunbun damammakin da za'a samu karkashin yarjejeniyar ciniki tsakanin kasashen nahiyar da kuma bangaren masu zuba jari daga ketare. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China