in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Netanyahu ya gargadi Hamas bayan karuwar tashin hankali a zirin Gaza
2018-10-15 14:13:13 cri
Firaiministan Israeli Benjamin Netanyahu ya gargadi kungiyar Hamas cewa idan ta ci gaba da kaddamar da hare hare kan Isra'ilan, to za a dakatar da harin ta hanyar da ba zai yiwa Hamas jin dadi ba.

Netanyahu ya yi wannan gargadi ne a lokacin taron majalisar zartaswar Isra'ilan a Jerusalem.

Firaiministan ya yi wannan gargadi ne a sakamakon karuwar tashe tashen hankula wanda Palestinawa ke tada boren a kusa da wani shingen jami'an tsaro dake zirin Gaza.

A ranar Juma'ar da ta gabata, wasu mutane 15,000 suka yi zanga zanga a kusa da shingen jami'an sojojin, inda suka kona tayoyi da kuma girke duwatsu a kan titi, kana da yin amfani da abubuwan fashewa da gurneti da suka dinga jefan dakarun tsaron Isra'ilan.

A lokacin boren, kamar yadda wata majiya daga Palestinawa ta rawaito, an kashe mutane 7 daga cikin masu zanga zangar, da suka hada da mutane 3 wadanda suka tsallaka shingen da dakarun sojojin Isara'ilan suka kafa. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China