in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria ta bukaci kasa da kasa su binciki laifukan yaki da Amurka ta jagoranta a kasarta
2018-10-15 10:06:06 cri

Ma'aikatar harkokin wajen Syrian ta bukaci kasa da kasa da su gudanar da bincike kan laifukan yaki da Amurka ta jagoranci kaddamarwa a kasar, kiran ya biyo bayan wani harin baya bayan nan ne wanda Amurka ta jagoranci wata tawagar mayaka a yankin Deir al-Zour, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya sanar.

Ma'aikatar ta kuma bukaci a kawo karshen abin da ta kira "cin zali" da "take hakki" sakamakon ci gaba da zaman da dakarun Amurka ke yi a Syria, in ji kamfanin dillancin labaran SANA.

"Yin amfani da haramtattun makamai a Syria ya sabawa dokar kasa da kasa da hakkin bil adama." in ji ma'aikatar harkokin wajen Syria.

Sanarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan da Amurka ta jagoranci wata tawagar hadin gwiwa, inda suka yi amfani da muggan makamai don kaddamar da hari a garin Hajin, daya daga cikin ragowar garuruwan dake hannun mayakan IS a gabashin lardin Deir al-Zour.

Ma'aikatar ta ce, an hallaka mutane masu yawa ko kuma jikkata wasu da dama a lokacin harin.

Gwamnatin Syria ta jima tana yin kiraye kirayen kawo karshen ci gaba da zaman dakarun hadin gwiwar Amurka dake Syria.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China