in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar kundin mulkin Kamaru za ta saurari korafin da aka nemi soke zaben shugaban kasar
2018-10-15 09:14:05 cri

A ranar 16 ga watan nan na Oktoba majalisar kundin tsarin mulkin Kamaru za ta fara sauraron karar da wasu 'yan takarar jam'iyyun adawa da masu jefa kuri'a suka shigar, inda suka bukaci a soke sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 7 ga watan Oktoba, sakatare janar na majalisar Malego Joseph Asse, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a jiya Lahadi.

Za'a fara sauraron karar ne da misalin karfe 11 na safe, agogon yankin a Yaounde, babban birnin kasar, in ji Asse.

A cewar hukumar zabe kasar Kamaru, wato (Elecam), an shigar da korafe korafe kimanin 25 wadanda masu jefa kuri'a da 'yan takara suke neman a soke wani bangare na zaben ko kuma ma a soke zaben baki daya.

Yan takarar neman shugabancin kasar da suka hada da Joshua Osih na babbar jam'iyyar adawa ta SDF, da Maurice Kamto na CRM, da kuma Cabral Libii na jam'iyyar UNIVERS, sun koka game da zaben, inda suka ce, an tafka kura kurai masu yawa, kuma zaben ya saba dokokin zaben Kamaru kamar yadda tawagogin sanya ido a zaben suka bayyana, in ji su.

A bisa dokar zaben kasar Kamaru, majalisar kundin mulkin kasar za ta sanar da sakamakon karshe na zaben ne a ranar 22 ga watan Oktoba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China