in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a bude Canton Fair karo na 124 a birnin Guangzhou
2018-10-14 16:54:40 cri

Bisa labarin da babban taron shiga da fitar da kayayyaki na kasar Sin, watau Canton Fair ya fidda, an ce, a ranar 15 mai zuwa, za a bude taron cinikin kasa da kasa din karo na 124 a babban dakin nune-nunen Canton Fair dake birnin Guangzhou na kasar Sin.

Kakakin Canton Fair Xu Bing ya bayyana cewa, ba a canja babban tsarin Canton Fair na wannan karo ba, za a gudanar da taron cikin lokuta guda uku, kuma gaba daya fadinsa zai kai muraba'in mita dubu 1185, akwai rumfunan nune-nune guda 60645, sa'an nan, kamfanonin kasar Sin da na ketare guda 25583 za su halarci taro na wannan karo.

An kafa yankunan nune-nunen hajojin ketare guda 6 a wannan karo, kuma fadinsu zai kai muraba'in mita dubu 20, gaba daya a akwai rumfunan nune-nune guda 998, inda kamfanonin ketare guda 637 wadanda suka zo daga kasashe da yankuna guda 34 za su halarci taron. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China