in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kaddamar da shirin yaki da samar da magungunan jabu da gurbatattun kayan abinci
2018-10-14 15:21:17 cri
Jami'an 'yan sandan kasar Sin sun kaddamar da shirin gangamin yaki da masu aikata laifukan da suka shafi samar da abinci marasa inganci, da magunguna da kayayyakin amfanin gona na jabu da sauran ayyukan dake gurbata muhalli.

Aikin gangamin na tsawon watanni uku an fara shi tun daga ranar 10 ga watan nan na Oktoba, zai shafi bankado kayan abinci da aka haramta amfani da su, da aikata zamba tare da yaudarar masu tallata kayayyaki da masu samar da magungunan jabu da kayayyakin kiwon lafiya ga mutanen dake fama da cututtuka masu wahalar magani kamar hawan jini da ciwon suga, ma'aikatar tabbatar da tsaron lafiyar jama'a ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce za'a yaki da masana'antu da 'yan kasuwar dake samarwa ko kuma sayar da magungunan jabu da marasa inganci da suka hada da maganin kashe kwari, da na adada kayan amfanin gona, da sinadarin hada takin zamani, da sauran kayayyakin amfani gona.

A cewarsa sanarwar, ayyukan da suka shafi gurbata muhalli na daga cikin abubuwan da za'a mayar da hankali kamar hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba, da kamun kifi tare da zubar da shara dake illa ga muhalli. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China