in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SCO: Ana nuna kin amincewa da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya
2018-10-13 16:50:49 cri


An rufe taro na 17 na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO na kwanaki biyu a birnin Dushanbe dake kasar Tajikistan. Masu halartar taron sun gabatar da hadaddiyar sanarwa bayan taron, inda suka jaddada cewa, ya kamata a zurfafa tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, da adawa da duk wata hanya ta ra'ayin ba da kariya ga cinikayya da zartar da ra'ayi na kashin kai. Kungiyar SCO ta sake jaddada ra'ayin tabbatar da cinikayya tsakanin bangarori daban daban cikin 'yanci.

A watan Yunin bana, an gabatar da hadaddiyar sanarwa ta kasashe mambobin kungiyar SCO game da samar da sauki kan cinikayya yayin taron koli na birnin Qingdao na kungiyar, inda aka yi kira da tabbatar da tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban bisa tushen ka'idojin kungiyar ciniki ta duniya wato WTO, da jaddada bukatar bangarori daban daban na son ci gaba da hadin gwiwa don samar da sauki kan ciniyakka da juna. Bayan watanni hudu, firaministocin kasashe mambobin kungiyar SCO sun sake gabatar da ra'ayi tare game da wannan batu, wadanda suka shaida ra'ayi iri daya na kasashe mambobin kungiyar.

A yayin taron Dushanbe, shugabanni ciki har da firaministan kasar Rasha Dimitri Medvedev sun yi Allah wadai da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya da ra'ayin yanke hukunci daga bangare daya da wasu kasashe suke yi. Wannan ya shaida cewa, kungiyar SCO tana kara taka muhimmiyar rawa wajen yaki da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya da tabbatar da tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban daban.

Abin da ya fi jawo hankali shi ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ba da shawarar kaddamar da yin bincike kan yankin yin ciniki cikin 'yanci na kungiyar SCO a gun taron na wannan karo, da kafa tsarin hadin gwiwar tattalin arziki a yankuna sannu a hankali. Hadaddiyar sanarwar da aka gabatar a gun taron a wannan karo ta amsa wannan kira, inda ta gabatar da cewa, bangarori daban daban su sa kaimi ga samar da sauki ga ciniki da zuba jari don cimma burin yin musayar kayayyaki da jari da hidima da fasahohi cikin 'yanci bisa mataki mataki.

Yawan mutanen kasashe mambobin kungiyar SCO ya kai kimanin rabin adadin mutanen dukkan duniya, da fadinsu ya kai fiye da kashi 60 cikin dari bisa fadin nahiyar Turai da Asiya, kana yawan alkalumansu na GDP ya zarce kashi 20 cikin dari bisa na dukkan duniya. Don haka, Abu ne mai wuya a kafa yankin ciniki cikin 'yanci bisa tushen wannan kungiya. Amma bisa yanayin bunkasuwar kungiyar, akwai wasu sharuda wajen yin bincike kan kafa yankin yin ciniki cikin 'yanci da kasar Sin ta gabatar.

Na farko, a fannin siyasa, kasashe mambobin kungiyar SCO na yin imani da juna a fannin siyasa, kuma shugabannin kasashen na mu'amala da juna sosai, da hadin gwiwa a fannoni daban daban. Kana kasashe mambobin kungiyar sun maida aikin raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a a matsayin aikin dake gaban komai, suna begen yin hadin gwiwa da juna.

Na biyu, bisa yanayin hadin gwiwar tattalin arzikinsu, kasashe mambobin kungiyar SCO za su samu moriya daga yin ciniki cikin 'yanci da hadin gwiwa a yankuna, kana suna nuna goyon baya a wannan fanni. Kasashe mambobin kungiyar suna yin mu'amalar ciniki sosai, kana su abokan cinikayya ne, sannan sun fadada ciniki da zuba jari a fannoni daban daban, wadda ke alamta kyakkyawar makoma kan hadin gwiwarsu.

Na uku, a fannin ka'idojin cinikayya, ban da kasar Uzbekistan, sauran kasashe mambobin kungiyar SCO, mambobi ne na kungiyar WTO, wadanda suke da tsarin ka'idojin cinikayya iri daya, kana suna da ra'ayi iri daya kan bin ka'idojin kungiyar WTO da aiwatar da ayyukan bisa ka'idojin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China