in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na kokarin inganta kwarewar yara mata wajen amfani da kafar Intanet
2018-10-12 14:19:46 cri

Jiya Alhamis, wato ranar 11 ga watan Oktobar bana, rana ce ta yara mata ta kasa da kasa, inda hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin gami da asusun kula da kananan yara na kasar suka shirya wani taron sanin makamar aiki dangane da wannan muhimmiyar rana a birnin Beijing. Wani rahoton da aka gabatar a wajen taron ya yi nuni da cewa, yaran kasar Sin na da kwarewa da basira wajen amfani da kafar sadarwar Intanet, amma duk da haka, suna fuskantar matsalolin da suka shafi rashin iya tantance abubuwan batsa dake Intanet, musamman ma yara mata.

A yayin taron sanin makamar aikin, asusun kula da kananan yara na kasar Sin ya bayar da wani rahoto kan nazarin kwarewa da basirar yara mata da iyali wajen amfani da kafar sadarwar yanar gizo ta Intanet a sabon zamanin da muke ciki, inda ya nuna cewa, kwarewa gami da basirar yara ta amfani da kafar Intanet ta kunshi fannoni daban-daban, ciki har da fasahohin amfani da shi, da kwarewar tantance abubuwan dake Intanet, da karfin yin rigakafin hadari, da kwarewar shawo kan matsala ta Intanet, tare kuma da kwarewar raya harkokin Intanet da sauransu. Rahoton ya ce, yaran kasar Sin na da kwarewa da basira wajen amfani da kafar Intanet, amma ba su da kwarewa wajen tantance abubuwan batsa ko abubuwa marasa kyau dake bazuwa a Intanet, musamman yara mata, wadanda suka fi jin radadi a jikinsu saboda hadarin dake cikin kafar Intanet.

A nasa bangaren, babban magatakardan asusun kula da kananan yara na kasar Sin Zhu Xisheng ya bayyana cewa:

"Yara mata sun fi dandana kudarsu sakamakon hadarurrukan dake kunshe cikin kafar sadarwar Intanet. Alal misali, adadin yara matan da suka taba gamuwa da matsalar abubuwan batsa ta Intanet ya kai kashi 29.3 bisa dari. Bugu da kari, adadin yara matan da suka taba funkantar zamba ta Intanet ya kai kashi 35.9 bisa dari, yayin da yawan wadanda suka taba gamuwa da matsalar cin zarafi ta Intanet ya kai 24.1 bisa dari. Muna iya cewa, duk da cewa kafar sadarwar yanar gizo ko Intanet na saukakawa yara al'amura, amma suna fuskantar babban hadari."

A cewar wannan rahoto, idan ana son karfafa kwarewa gami da basirar yara mata ta fannin amfani da Intanet, ba ma kawai ya kamata a fadakar da yaran su kansu ba, har ma dole a himmatu wajen kyautata yanayin da iyali da ma al'umma ke ciki. A halin yanzu, makarantu da iyalai a kasar Sin ba su yin hadin-gwiwa da mu'amala sosai wajen fadakar da yara kan dabarun amfani da kafar sadarwar Intanet. Mista Zhu Xisheng ya yi karin hasken cewar:

"A wani bangare, makarantun kasar Sin ba su koyar da dalibai sosai ba game da hanyoyin amfani da kafar Intanet. Alal misali, yawancin lokuta, yara mata suna makaranta, amma makarantu daban-daban, ko firamare, ko midil, ko kuma sakandare, ba su koyar da yara mata ilimin da ya jibanci Intanet sosai ba, ko a cikin aji, ko kuma bayan an tashi daga makaranta, wannan babbar matsala ce. A dayan bangaren kuma, duk da cewa iyaye a kasar Sin na sa ido sosai kan 'ya'yansu game da harkokin amfani da Intanet, amma ba su yi musu jagora. A akasarin gidajen Sinawa, iyaye kan maida hankalinsu kan sa ido gami da takaitawa yaransu amfani da kafar Intanet, wato su kan gaya musu abubuwan da ya kamata su yi da abubuwan da bai kamata su yi ba, maimakon su rika yi musu jagora wajen amfani da Intanet."

Saboda haka, rahoton ya shawarci hukumomin gwamnati, da kamfanonin Intanet, da iyalai da kuma makarantu daban-daban da su hada kai, domin kirkiro wani yanayin amfani da Intanet da ya dace ga yara mata. A wajen wannan taron sanin makamar aiki, wakilai daga bangarori daban-daban sun yi kira da a dauki matakan kare yara mata don tsabtace tsarin amfani da kafar sadarwar Intanet.

A nata bangaren, mataimakiyar shugaban haddadiyar kungiyar mata ta kasar Sin, Madam Huang Xiaowei ta bayyana cewa:

"Ya kamata mu tabbatar da doka da oda a kafar sadarwar Intanet, da sa wa bayanan Intanet rukunoni daban-daban, da kara ba wa yara jagora da sa musu ido wajen amfani da Intanet, tare kuma da kara karfin yaki da masu aikata laifin keta hakkin yara musamman yara mata ta kafar Intanet, don kara ba su kariya. Bugu da kari, ya kamata mu samu hadin kai tsakanin makarantu da gidaje gami da unguwanni, da gudanar da ayyukan fadakarwa game da hanyoyin amfani da Intanet, da karfafa gwiwar bangarori daban-daban ta yadda za su kara kokarin tabbatar da tsaro a kafar Intanet."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China