in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNSC ta bukaci a daidaita takaddamar kan iyakokin Sudan da Sudan ta kudu
2018-10-12 09:53:39 cri
Kwamitin sulhun MDD ya yanke shawarar tsawaita wa'adin ayyukan wanzar da zaman lafiya a yankin Abyei da ake takaddama kansa muddin kasar Sudan da makwabciyarta Sudan ta kudu suka gaza daidaita sabanin dake tsakaninsu game da shata kan iyakokin kasashen.

A kuri'ar da aka kada wanda ta samu amincewar dukkan mambobin kwamitin MDDr kan kudirin doka mai lamba 2438, kwamitin MDDr ko kuma UNISFA, zai tsawaita wa'adin aikin wanzar da zaman lafiyar zuwa ranar 15 ga watan Afrilun 2019 a yankin na Abyei da ake takaddama kansa tsakanin Sudan da Sudan ta kudu, idan har kasashen biyu suka cigaba da jan kafa wajen gaza samar da gagarumin cigaba na warware rikicin kan iyakokin nasu.

A cewar daftarin, ana saran Sudan da Sudan ta kudu zasu dauki wasu matakai guda 7 nan da watanni 6 masu zuwa, game da batun shata kan iyakokin nasu, wanda ya kunshi bada 'yancin zirga-zirgar jami'an kiyaye zaman lafiya na UNISFA, da fara aiwatar da tantance sassa 10 na iyakokin kasashen biyu don bada damar zirga zirgar alummominsu, da kuma gudanar da tattaunawa a kalla sau biyu na hukumar hadin gwiwa mai kula da kan iyakokin kasashen da kuma kwamitin shata kan iyakokin kasashen biyu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China