in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yaba da matsayin Canada na rashin lalata muradun sauran kasashe
2018-10-11 18:46:23 cri

Yau Alhamis yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijjing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kasar Sin ta yaba da matsayin da matakan kasar Canada na rashin kawo illa ga 'yanci da muradun sauran kasashe.

Jami'in ya kara da cewa, har kullum kasar Sin ta nace ga manufar gudanar da cinikayya maras shinge, tana kuma goyon bayan tsarin cinikayya tsakanin bangarori da dama karkashin jagorancin hukumar cinikayya ta duniya, haka kuma ta nuna adawa da duk wani nau'i na ba da kariya ga harkokin cinikayya, da kuma matakan da aka dauka bisa ma'auni iri biyu.

Kasar Sin tana fatan za a gudanar da cinikayya a shiyoyi daban daban bisa ka'idar yin hakuri da juna ba tare da wata rufa rufa ba, ta yadda za a samar da yanayin cikayayya mai inganci a fadin duniya, tare kuma da samar da moriya ga daukacin al'ummun kasashen duniya baki daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China