in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin Na Kafa "Tarkon Cin Bashi" Ne Ko Samar Da Damar Samun Bunkasuwa
2018-10-11 18:12:09 cri

A kwanakin baya, mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya gabatar da wani jawabi, inda ya zargi kasar Sin da ta samar da rancen kudi fiye da dala biliyan 100, don gina ayyukan more rayuwa a nahiyar Asiya, da Afirka, da Turai, da Latin Amurka, wanda ya zamewa wasu kasashe masu tasowa "tarkon cin bashi". Ya bayyana cewa, kasar Amurka za ta samar da wani sabon zabi da zai iya maye gurbin kasar Sin.

Bisa yanayin tsanantar rikicin ciniki a tsakanin Sin da Amurka, jawabin Pence ya sake zargi kasar Sin ba tare da tushe ba. Kasar Sin ba ta yiwa wasu kasashe masu tasowa "tarkon cin bashi" ba, maimakon hakan bari mu yi kidaya game da wannan.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, kafofin watsa labarai na kasashen yamma su kan ambata Sri Lanka yayin da suke watsa labarai game da "tarkon cin bashi". Pence ya ce, kasar ta Sri Lanka ta gamu da matsalar cin bashi mai yawa ne sakamakon wani kamfanin dake karkashin mallakar gwamnatin kasar Sin, wanda ya gina wata tashar ruwan teku wato Bambantota a kasar wadda kila ne ba ta da amfanin kasuwanci ko kadan, an ce, kasar Sin ta matsa lamba ga kasar Sri Lanka, inda ta bukaci gwamnatin Sri Lanka da ta mika wannan sabuwar tashar ruwan teku ga hannun Sinawa kai tsaye, kila ne tashar za ta kasance sansanin aikin soja na sojojin teku na kasar Sin cikin sauri.

Hakika dai, bisa alkaluman da babban bankin kasar Sri Lanka ya samar, an ce, adadin rancen kudin da kasar ta samu daga kasar Sin ya kai kaso 10 bisa dari kawai dake cikin kwatankwacin bashin waje na kasar, wadanda a ciki, kasar Sin ta ba ta gatanci har kaso 61.5 bisa dari. Kan wannan, a fili ne firayin ministan Sri Lanka Wickremesinghe ya bayyana cewa, kasarsa ba ta gamu da matsalar cin bashi domin kasar Sin ba, gwamnatin kasar da kamfanin kasar Sin sun daddale yarjejeniyar kula da harkokin tashar ruwan tekun Bambantota ne bisa tushen zaman daidai wa daida da moriyar juna, makasudin da aka gina tashar nan shi ne domin ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sri Lanka.

An yi hasashen cewa, zuwa shekara ta 2020, yawan kudin shigar da wannan mashigin teku ya samu zai kai kashi 40 bisa dari na jimillar kudin shigar da gwamnatin Sri Lanka za ta samu, kana, zai samar da guraben ayyukan yi dubu goma kai-tsaye, gami da dubu sittin da ba na kai-tsaye ba. Masu amfani da kafar Intanet na kasar Sri Lanka na ganin cewa, wannan aiki yana da kyau sosai, wanda zai kawo moriya da alfanu ga kasar.

Irin wannan muhimmin aikin dake kawowa Sin da Sri Lanka moriya duka, ya zama wani nau'in cinikin da wata kasa ta tilastawa wata kasa ta daban don ta yi, har ma an sanya harkokin soja a ciki. Wannan ra'ayi na Mike Pence, ra'ayi ne na nuna fin karfi, kana, ra'ayinsa ne kawai ba na saura ba. Sanin kowa ne, Amurka na da sansanonin soja sama da dari takwas a kasashe sama da saba'in a duk fadin duniya, al'amarin da ya sa take tsammanin cewar akwai harkokin da suka shafi soja ne a cikin hadin gwiwar sauran kasashen duniya.

Ban da kasar Sri Lanka, kuma kasashen yamma sun kara da kasashen Pakistan, Philippines, Venezuela, Djibouti, Papua New Guinea na wai sun fada cikin "tarkon cin bashi" da kasar Sin ta haka. Kasashen din dai suna da halin musamman na bai daya, wato dukkansu suna son gudanar da hadin kai tare da kasar Sin kan ayyukan dake shafar shawarar "Ziri daya da hanya daya".

A hakika dai, kowane aikin hadin kai da kasar Sin ta gudanar tare da kasashe masu tasowa bisa manufar yin hadin gwiwar tuntubar juna, da ginawa tare da raba moriya, dama ce mai kyau wajen samun ci gaba. Ya zuwa watan Satumba na bana, kasar Sin ta riga ta sa hannu kan takardun hadin kai a tsakanin gwamnatoci guda 149 tare da kasashe 105 dake shafar shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kungiyoyin kasa da kasa guda 29. A tsakanin shekarun 2013 da 2017, jimilar kudin da aka samu wajen shige da fice a tsakanin Sin da kasashen dake shafar shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta kai RMB biliyan 33,200, matsakaicin karuwar kudin ya kai kashi 4 cikin 100 a kowace shekara.

Don haka, wadancan kasashen da kasar Amurka ta bayyana cewa, sun shiga "tarkon cin bashi" na kasar Sin, sun yi musu kan batun. Ministan harkokin wajen kasar Philippines Alan Peter Cayetano ya ce, adadin rancen kudin da kasar Philippines ta samu daga wajen kasar Sin, ya kai kashi 1 bisa dari na dukkanin rancen kudin da kasar ta samu, kasarsa ba za ta shiga "tarkon cin bashi" sakamakon rancen kudin da kasar Sin ta ba ta ba. A nasa bangare kuma, ministan harkokin tattalin arziki da sha'anin kudi na kasar Djibouti Ilyas Moussa Dawaleh ya nuna cewa, "babu wanda zai yi damuwa kan zuba jarin da kasar Sin, ko kuma sauran kasashen duniya suka yi a kasarsa ba, sabo da gwamnatin kasar ita kanta ta yanke shawara kan yadda za a raya kasa, babu la'akarin wannan batu da harkokin siyasar kasashen duniya." Haka kuma, shugaban bankin hanyar siliki na kasar Djibouti ya ce, "kasar Amurka ta riga kasar Sin shiga kasuwannin kasar Djibouti, amma, ya zuwa yanzu, mene ne ta taba yi wajen taimakawa kasar Djibouti? Kusan babu komai."

Yayin da kasashen Sin da Amurka ke yunkurin neman hadin kai da wasu kasashen ketare, idan aka kalli yadda kasar Sin ta taimaka wa kasashe masu tasowa, za a kara fahimtar wasu "muhimman ka'idoji guda biyar" da shugaba Xi Jinping ya jaddada, yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka, wato kasar Sin ba za ta tsoma baki kan yadda kasashen Afirka ke neman hanyar ci gabansu bisa halin da suke ciki ba, ba za ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, haka kuma ba za ta tilasta musu amincewa da ra'ayoyinta ba, ba za kuma ta gindaya musu ko wane irin sharadi na siyasa ba yayin da take samar wa Afirka taimako, kana ba za ta nemi muradu a siyasance ba yayin da take zuba jari ga Afirka.

Kasar Sin ta samar da kasashen Afirka wadannan manufofi, haka kuma za ta yi a sauran kasashe! (Marubuciya: Sheng Yuhong; Masu Fassarawa: Zainab Zhang, Jamila Zhou, Murtala Zhang, Bilkisu Xin, Kande Gao, dukkansu ma'aikatan CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China