in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin zai ci gaba da bunkasuwa cikin yanayin zaman karko
2018-10-11 13:39:06 cri

Kwanan baya, mataimakin shugaban kwamitin rayawa da yin kwaskwarimar kasa ta Sin, kana shugaban hukumar kididdigar kasa ta Sin, Ning Jizhe ya bayyana cewa, ko da a halin yanzu, ana fuskantar da wasu kalubaloli a fannin raya tattalin arziki cikin gida da kuma cikin kasashen ketare, amma tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da bunkasuwa cikin yanayin zaman karko. Ya kara da cewa, takaddamar cinikin dake tsakanin Sin da Amurka, ba za ta bata tsarin tafiyar da harkokin tattalin arziki a kasar Sin ba.

Ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana:

Bisa labarin da aka samu, an ce, wasu mizanin tattalin arziki na kasar Sin sun ragu a wasu watanni na shekarar bana. Dangane da wannan lamari, shugaban hukumar kididdigar kasar Sin Ning Jizhe ya yi bayani cewa, mizanin suna karuwa da raguwa a bisa al'ada, ba abin mamaki ba ne, kuma bisa nazarin da aka yi kan tattalin arzikin kasar Sin daga watan Janairu zuwa watan Agusta na bana, ana ganin cewa, an ci gaba da tafiyar da harkokin tattalin arzikin kasar Sin cikin yanayin zaman karko. Kana, cikin farkon watanni shida na shekarar bana, tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kashi 6.8 bisa dari, lamarin da ya nuna mana cewa, cikin watanni 36 da suka gabata, tattalin arzikin kasar Sin ya yi ta bunkasuwa cikin sauri. Haka kuma, mizanin farashin kayayyaki da na samun guraben aikin yi suna karuwa cikin yanayin zaman karko. Ya ce,"A fannin samar da guraben aikin yi kuma, daga watan Janairu zuwa watan Agusta na shekarar bana, adadin mutanen da suka samu ayyukan yi a biranen kasar Sin ya kai kimanin miliyan 10. Sannan daga watan Janairu zuwa watan Agusta na shekarar bana, farashin kayayyakin yau da kullum da mazauna ke bukata ya karu da kashi 2 bisa dari, adadin bai kai hasashen da aka yi a farkon shekarar bana ba, watau kashi 3 bisa dari."

Haka zalika ya ce, a halin yanzu, kasar Sin tana samun daidaito a harkokin cinikayyar duniya. Kana, adadin musayar kudaden da Sin ta adana ya kai sama da dallar Amurka biliyan dubu 3, kuma farashin musayar kudin Sin yana cikin yanayi na zaman karko. Bisa nazarin da aka yi a fannonin karuwar tattalin arziki, samun guraben aikin yi, farashin kayayyaki da kuma cinikayyar duniya, ana iya tabbatar da cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana bunkasuwa cikin yanayin zaman karko.

A sa'i daya kuma, Ning Jizhe ya bayyana cewa, riba ta fuskar tattalin arzikin kasar Sin tana karuwa, bisa kyautatuwar tsarin tattalin arzikin kasar. Ya ce, a halin yanzu, kasuwannin sha'anin kudi da na hajoji na kasa da kasa suna fuskantar kalubale da dama, lamarin da ya haifar da tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin, sakamakon babban la'akarin dake tsakanin tattalin arzikin Sin da na duniya. Amma, yana ganin cewa, tattalin arzikin Sin zai ci gaba da bunkasuwa cikin zaman karko, yana mai cewa, "Kasar Sin tana da dabarar fuskantar kalubalolin tattalin arziki, za ta kuma iya cimma babban burinta na samun bunkasuwar tattalin arziki, watau samun karuwar tattalin arziki na kashi 6.5 bisa dari a shekarar bana."

A halin yanzu, yanayin tattalin arzikin ketare ya canja sosai, kana sakamakon takaddamar cinikin da kasar Amurka ta haifar ya haddasa illa ga bunkasuwar tattalin arzikin Sin, amma, Mr. Ning ya ce, ba zai bata tsarin tafiyar da harkokin tattalin arziki na kasar Sin ba.

Idan aka tsokaci kan tasirin da takaddamar cinikin ya yi wa karuwar tattalin arzikin Sin, za a gane cewa, bisa kwaskwarimar da Sin ta yi a fannin tattalin arziki, goyon bayan da bukatun al'ummomin kasa ke nuna wa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da karuwa. Kuma karuwar bukatun al'umma da harkokin zuba jari za su ba da gudummawa matuka wajen raya tattalin arzikin kasar, yayin da rage tasirin da takaddamar cinikin ya yi wa tattalin arzikin Sin.

A fannin samar da guraben aiki yi kuma, ko da karin harajin kwastam ya haddasa raguwar odar da kamfanonin Sin suka samu, wanda ya haddasa illa ga batun samar da guraben aikin yi. Amma kasar Sin za ta iya warware wannan matsala ta hanyar zurfafa kwaskwarima a gida, yayin da gabatar da manufofin da za su sa kaimi ga al'ummomin kasar da su kafa kamfanoni da dai sauransu.

A fannin farashin kayayyaki kuma, Ning Jizhe ya ce, kasar Sin tana da cikakken tsarin masana'antu a nan duniya, ana iya samar da isassun kayayyakin gona da na masana'antu, sa'an nan, sana'o'in ba da hidima suna ci gaba da samun bunkasuwa a kasar.

Bugu da kari, a fannin tasirin da takaddamar cinikin ya yi wa kasar Sin a fannin samun daidaito kan harkokin cinikin duniya, Mr. Ning yana ganin cewa, a halin yanzu, kasar Sin tana samun rarar kudin cinikin duniya a fannin cinikin hajoji, yayin da samun gerar kudin cinikin duniya a fannin cinikin ba da hidima, gaba daya tana samun rarar kudin cinikin duniya. Shi ya sa, kasar Sin tana da karfi da kuma fasahohi na tabbabar da daidaito a harkokin cinikin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China