Babbar tashar samar da wutar lantarki bisa karfin haske gami da zafin rana ta farko a kasar Sin ta fara aiki
Babban kamfanin samar da makamashi mai tsabta mai suna CGN na kasar Sin ya sanar jiya Laraba cewa, tashar samar da wutar lantarki bisa karfin haske gami da zafin rana ta farko a kasar, wato tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 50, wadda kamfanin ya gina a birnin Delingha dake lardin Qinghai ta fara aiki, al'amarin da ya sa Sin ta zama kasa ta takwas, wadda ke da muhimmiyar fasahar samar da wutar lantarki bisa haske da kuma zafin rana a duk fadin duniya.
An ce, tashar Delingha za ta iya samar da wutar lantarki ba tsayawa har ta tsawon sa'o'i 24.(Murtala Zhang)