in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Erdogan ya shawarci kasashen Afirka da su rika amfani da kudaden su na gida yayin cinikayya da kasar sa
2018-10-11 09:36:40 cri
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya shawarci kasashen Afirka, da su rika cinikayya da kudaden kasashensu, a duk lokacin da suke hada hadar kasuwanci da kasar sa.

Kafar watsa labarai ta Anadolu, ta rawaito shugaban na Turkiyya na bayyana hakan a jiya Laraba, yayin taron dandalin bunkasa hada hadar cinikayya tsakanin Turkiyyar da kasashen Afirka.

Shugaban na Turkiyya dai ya jima yana zargin wasu manyan kasashen duniya, bisa abun da ya kira harin tattalin arziki da suke kaiwa kasar sa, matakin da ya yi matukar lahanta karfin kudin kasar lira.

Shugaba Erdogan, ya ce "Mun shirya daukar matakan bunkasa kawance ta fuskar tattalin arziki, ta hanyar amfani da kudaden kasashenmu, ba wai kawai yayin cinikayya da manyan abokan huldarmu ba, har ma a hada hadar mu da kawayenmu na nahiyar Afirka.

A wani jawabin da ya gabatar cikin watan da ya gabata, shugaban na Turkiyya, ya ce dogaron da kasarsa ke yi kan dalar Amurka, sannu a hankali na kara zama wani nauyi, maimakon hanyar samun sauki, yana mai cewa, mummunan tasirin da hakan ya yi ga tattalin arzikin kasarsa ya isa misali dake tabbatar da hakan. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China