in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi da takwaransa na Angola sun tsai da kudurin ciyar da huldar kasashensu gaba
2018-10-10 11:15:32 cri

Jiya Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Angola Manuel Lourenso, wanda ke yin ziyarar aiki a nan birnin Beijing, inda suka daddale yarjejeniyar hadin gwiwar dake tsakanin kasashensu.

Yayin shawarwarin da suka yi, shugabannin kasashen biyu wato Sin da Angola, sun cimma matsaya guda kan batun ciyar da huldar dake tsakanin kasashensu gaba.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, "Ina farin ciki matuka saboda na samu damar sake ganawa da shugaba Manuel Lourenso bayan wata guda kacal, da kammala taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a nan birnin Beijing. Ina maraba da zuwanka nan kasar Sin domin ziyarar aiki."

A yammacin jiya Talata 9 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Angola Manuel Lourenso, sun yi shawarwari a tsakaninsu a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing. Shugaba Lourenso ya sauka nan Beijing ne a ranar 8 ga wata, domin fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Sin. Shugabannin biyu dai sun taba ganawa da juna, yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, wanda aka kammala a nan birnin Beijing, wata guda kacal da ya gabata. Shugaba Lourenso shi ne shugaban kasar waje na farko wanda shugaba Xi ya karbi bakuncin sa, bayan bikin murnar kafuwar kasar Sin wato ranar 1 ga watan Oktoba.

Lokacin da suka fara yin shawarwari, shugabannin biyu sun tabo magana kan taron kolin dandalin tattaunawa hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar ba da dadewa a nan birnin Beijing. Shugaba Xi ya bayyana cewa, "Yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a watan jiya, gaba daya sassan biyu wato Sin da Afirka sun yarda cewa, za su yi kokari tare, domin kafa kyakkyawar makomar al'ummun Sin da Afirka, tare kuma da ingiza hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya. Kana sassan biyu za su kara mai da hankali kan aikin aiwatar da muradu takwas da aka tsara, tare kuma da goyon bayan manufar yin cinikayya tsakanin bangarori da dama, ta yadda za su gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu a sabon zamanin da ake ciki yadda ya kamata. Taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a Beijing cikin nasara, ya sa kaimi kan ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Angola. Haka kuma ya samar da sabbin damammaki ga sassan biyu, na tabbatar da cewa, ziyarar aikin da shugaba Lourenso ke yi a nan birnin Beijing, za ta ciyar da huldar dake tsakanin kasashen biyu gaba, za ta kuma kawo moriya ga al'ummun kasashen biyu."

Yayin shawarwarin, Xi ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Angola su kara karfafa amincewa juna, da fahimtar juna a fannin siyasa, haka kuma su kara karfafa cudanyar dake tsakanin manyan jami'an kasashen biyu. Kasar Sin ta fahimci tarihin ci gaban kasashen Afirka sosai, a don haka take goyon bayan kokarin da al'ummun kasashen Afirka suke yi, domin nuna adawa da tsoma bakin da sauran kasashen duniya suke yi wa harkokin gidan kasashensu, tare kuma da samun ci gaba yadda ya kamata. Xi ya yi nuni da cewa, kamata ya yi sassan biyu su yi kokarin aiwatar da nasarorin da aka cimma, yayin taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ban da haka kuma, yana fatan sassan biyu za su kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu a fannonin al'adun gargajiya da masana'antu, ta yadda za su samu moriya tare.

A nasa bangare, shugaba Lourenso ya bayyana cewa, cudanyar dake tsakanin manyan jami'an kasashen biyu ta nuna cewa, sassan biyu suna mai da hankali matuka kan huldar dake tsakaninsu, kasarsa tana fatan sassan biyu za su kara karfafa hadin gwiwa a fannin gina kayayyakin more rayuwar jama'a, da inganta rayuwar al'ummar kasar, ta yadda kasar Angola za ta samu ci gaba bisa taimakon kasar Sin.

Shugaba Lourenso ya kara da cewa, Angola tana ba da muhimmanci kan babban tasirin da kasar Sin ke kawowa kasa da kasa, ita ma tana matukar darajanta babbar rawar da Sin take takawa, yayin da ake daidaita matsalolin da kasashen Afirka ke fuskanta. Hari la yau Angola tana goyon bayan manufar gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama, tana kuma ganin cewa, ya dace kasashen duniya su tsai da kuduri tare kan makomar duniya, kuma tana fatan za ta kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin daga duk fannoni. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China