in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jefa kuri'u a zaben shugaban kasar Kamaru dake yamma maso tsakiyar Afirka
2018-10-09 14:00:02 cri

A ranar 7 ga wata, an jefa kuri'u a zaben shugaban kasar Kamaru dake yamma maso tsakiyar Afirka, shugaba Paul Biya na yanzu, mai shekarun haihuwa 85, wanda ya riga ya shafe shekaru 36 yana shugabancin kasar na cikin 'yan takarar zaben, inda yake neman wa'adin aiki a karo na 7.

An soma jefa kuri'u a zaben shugaban kasar ta Kamaru a ranar 7 ga wata da karfe 8 na safe. 'Yan takara 8, ciki har da shugaban kasar na yanzu Paul Biya sun shiga zaben. Masu jefa kuri'a kusan miliyan 6.6 sun jefa kuri'arsu a rumfunan zabe kimanin dubu 26 a duk fadin kasar, ciki kuwa rumfuna dubu 3 suna yankunan da ake amfani da Turanci dake kudu maso yammacin kasar, da na arewa maso yammacin kasar, wadanda ke fama da tashin hankali.

Baya ga haka, masu jefa kuri'a kimanin dubu 19 dake kasashen ketare sun jefa kuri'arsu a rumfuna 66 dake ketare. An kuma karfafa matakan tsaro a kewayen wasu gine-ginen gwamnati, da muhimman manyan kayayyakin more rayuwa na kasar, da nufin ba da tabbaci ga gudanar da aikin jefa kuri'a yadda ya kamata. Ana iya ganin masu jami'ai dauke da bindigogi a yawancin rumfunan jefa kuri'a. Kana ana iya ganin masu sa ido na wasu kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da kungiyar AU.

A ranar 5 ga wata, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, ya kamata a gudanar da zaben na Kamaru cikin zaman lafiya, wanda kuma zai kunshi kowa da kowa.

A wannan ranar, an rufe kan iyakokin kasar ta Kamaru, a sa'i guda kuma, an haramta duk wani nau'i na ayyukan gudanarwa, da kai da kawowa na mutane da kayayyaki a tsakanin birane. A cikin sanarwa ta farko da babban jami'in zabe na kasar Essosse Erik ya bayar bayan awoyi 3 da fara jefa kuri'a, ya ce an gudanar da zaben shugaban kasar a wannan rana yadda ya kamata, kuma babu rahoto game da aukuwar wani hali na musamman. Amma akwai labari na cewa, an harbe 'yan aware guda 3 har lahira, a hedkwatar yankin arewa maso yammacin kasar sakamakon kokarin gurgunta zaben. Kafin hakan, kungiyoyin 'yan aware dake yankuna masu amfani da Turanci dake kudu maso yammaci, da arewa maso yammacin kasar sun taba barazanar cewa, za su hana jefa kuri'a a yankunan biyu.

Yarukan hukumar kasar Kamaru su ne Faransanci da Turanci, kuma mazauna yankuna masu amfani da Turanci dake kudu maso yammaci, da arewa maso yammacin kasar sun kai kashi 1 cikin 5, na daukacin mutanen kasar baki daya. A cikin shekaru biyu da suka wuce, an yi ta samun tarzoma a yankunan, har ta kai ga rikici da makamai, inda wasu 'yan aware masu tsattsauran ra'ayi ke fafata rikici tsakaninsu da dakarun tsaron kasar, hakan ya sa mutane da yawa suka rasa gidajensu.

Bisa wannan yanayin da ake ciki ne aka shirya zaben shugaban kasar. Paul Biya mai shekaru 85, dan takara na jam'iyyar RDPK mai rike mulkin kasar, kuma shugaban kasar na yanzu, da ya rike mulkin kasar har shekaru 36, shi ma ya shiga zaben don neman wa'adin aikinsa na 7, wannan ma ya jawo hankalin mutane a wannan babban zaben na kasar ta Kamaru.

An haifi Paul Biya a watan Faburairu na shekarar 1933, a jihar Kudu ta kasar Kamaru, yana bin darikar Catolika ta addinin kirista, ya kuma taba kara yin karatu a kasar Faransa a lokacin yana matashi. A watan Yuni na shekarar 1975 ya dare kujerar firaministan kasar, a watan Nuwamba na shekarar 1982 ya zama shugaban kasar. Daga baya kuma, ya ci gaba da zarcewa a kujerar shugaban kasa a jere, a shekarar 1984, 1988, 1992, 1997, 2004 da kuma 2011.

A nasa bangaren kuwa, dan takarar jam'iyyar SDF Joshua Osih, jam'iyyar adawa da ta fi girma a kasar Kamaru, zai samu rinjaye a yankuna masu amfani da Turanci dake kudu maso yammaci, da arewa maso yammacin kasar.

Bisa dokar zaben ta Kamaru, an shirya zaben shugaban kasar ne ta hanyar jefa kuri'a kai tsaye, wanda ya samu kuri'u mafi yawa ne zai lashe zaben, kuma ko wane wa'adin aikin shugaba na da tsawon shekaru 7, kuma ana iya neman ci gaba da zama shugaban. Kwamitin kundin mulkin kasa zai sanar da sakamakon zaben ne cikin kwanaki 15 bayan jefa kuri'a. Kafofin watsa labaru na ganin cewa, ana sa ran Paul Biya zai ci gaba da samun nasara. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China