Kwamitin na IOC ya yanke wannan shawara ne, a zaman sa na 133, wanda hakan ke nuna cewa, Senegal ce kasar Afirka ta farko da za ta karbi bakuncin gasar Olympic.
Kafin yanke wannan shawara, kasashen Botswana, da Najeriya, da Senegal da Tunisia, sun gabatar da bukatar su ta karbar bakuncin gasar. To sai dai kuma bayan duba na tsanaki, hukumar zartaswa, da jagororin IOCn, sun gamsu cewa Senegal ce mafi dacewa da gasar.
Da yake tabbatar da hakan, shugaban IOC Thomas Bach, ya ce kasashen Afirka sun goyi bayan Senegal, bisa bukatarta, ta karbar bakuncin wannan gasa dake tafe a shekarar 2022. Ya ce Senegal na da tarin matasa, da kuma sha'awar wasanni, don haka wannan dama ce ga Afirka, kuma dama ce ga kasar Senegal.
Biranen kasar uku da suka hada da fadar mulkin ta wato Dakar, da sabon birnin Diamniadio, da kuma birnin Saly na bakin ruwa ne za a yi amfani da su, wajen gudanar da wannan gasa. (Saminu Alhassan)