in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libiya: Sama da 'yan gudun hijira 192,000 na bukatar tallafi
2018-10-09 10:21:14 cri
Hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta MDD ko UNHCR a takaice, ta ce a halin da ake ciki, yawan 'yan gudun hira da suka tserewa muhallan su, suke kuma bukatar tallafin jin kai a cikin kasar Libiya ya haura mutum 192,000.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce al'ummun da tashe tashen hankula suka raba da muhallan su a Libiyan na bukatar karin taimako, wanda zai ba su damar komawa gidajen su da zarar damar hakan ta samu.

Bisa jimilla, yawan al'ummun da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira na cikin kasar Libiya ya kai mutum 192,513, wadanda kuma UNHCR ke baiwa tallafi.

Hukumar dai na samar musu da taimakon kayayyakin da ba na abinci ba, da kudin kashewa. Tana kuma ba da agaji wajen aiwatar da ayyukan da ke yin kyakkyawan tasiri ga rayuwar su.

Mahukuntan kasar Libiya, tare da hukumomin kasa da kasa, sun cimma nasarar warware wasu tarin matsaloli, da masu samun mafaka a cikin kasar ke fuskanta a cikin shekaru masu yawa, a lokacin da kuma tashe tashen hankula, da yaki tsakanin sassan kungiyoyi masu dauke da makamai, ke kara yawan masu gudun hijira a sassan biranen kasar masu yawa. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China