in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci hadin gwiwar gwamnati da hukumomi masu zaman kansu don inganta fannin lafiya a Africa
2018-10-09 10:16:16 cri
Masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya sun bukaci hadin gwiwar gwamnati da hukumomi masu zaman kansu don bunkasa fannin lafiya a nahiyar Afrika.

A wani taron karawa juna sani na masu ruwa da tsakin a fannin kiwon lafiya na Afrika wanda aka gudanar a Johannesburg, ministan lafiyar kasar Afrika ta kudu Aaron Motsoaledi, ya ce kudurin samar da kiwon lafiya ga kowane bil adama nan da shekarar 2020 wani muhimmin batu ne da zai rage wahalhalun da ake fama dasu a tsarin kiwon lafiyar Afrika.

Yace kasar Afrika ta kudu tana kokarin aiwatar da shirin inshorar lafiya, ya kara da cewa, gwamnati tana bukatar samun cikakkun kudaden gudanarwa domin duka bangarori na masu kudi da talakawa su samu damar amfana daga tsarin kiwon lafiya mai inganci.

Kwamishiniyar sashen kula da walwalar jama'a ta kungiyar tarayyar Afrika Amira Elfadil, ta ce hadin gwiwar bangaren gwamnati da hukumomi masu zaman kansu muhimmin batu ne, muddin dai ana son cimma nasarar kyautata fannin kiwon lafiya a nahiyar.

"Kyautata bangarori masu zaman kansu muhimman batu ne wajen cimma nasarar kiwon lafiya da samun dawwamamman cigaba. Babu bukatar a samu rarrabuwar kawuna a tsarin wanda zai iya haddasa rudani a hasarar dukiya" in ji ta.

Ministoci da wakilan hukumomin lafiya daga kasashen Afrika daban daban ne suka bayyana irin nasarorin da suka samu karkashin tsare tsaren da suka aiwatar. Da dama daga cikinsu sun bukaci a yi amfani da sabbin fasahohin zamani, wasu kuma suna ganin samar da gwamnati mai tsabta da kuma yakar rashawa a fannin kiwon lafiyar shi ne mafita. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China