Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwaransa na Amurka
2018-10-08 15:25:45
cri
Mamba a majalisar gudanarwa kasar Sin kana Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo dake ziyara a kasar Sin, inda ya ce ya kamata kasar Sin da Amurka, su bi hanya madaidaiciya ta hadin gwiwar moriyar juna maimakon shiga rikici da juna da yin fito-na-fito. (Fa'iza Mustapha)