in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar matsayin yawon shakatawa na Sinawa ta nuna amincewarsu a kan makoma
2018-10-08 14:27:14 cri

Yawon shakatawa muhimmin zabi ne na Sinawa a lokacin hutu na murnar cika shekaru 69 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin na mako guda. Bisa kididdigar da aka yi, a wannan lokacin hutu na bana, Sinawa da yawa ba su gamsu kan cin abinci da sayen kayayyaki kawai ba, a maimakon haka, sun fi sha'awar kashe kudi kan karfafa ilminsu a fannin al'adu. Ban da wannan kuma, yawan Sinawa da suka zabi kasashen ketare don yin yawon shakatawa ya kuma karu. Kwararru suna ganin cewa, neman yawon shakatawa mai inganci da Sinawa ke yi, ya nuna amincewarsu a kan al'adu da makomar kasarsu a nan gaba.

A lokacin hutu na bikin kasa, Sinawa da yawa sun kai ziyara a wasu shahararrun wuraren yawon shakatawa da gidajen adana kayayyakin tarihi, don fahimtar al'adun kasar Sin na dogon tarihi. Da ma yawancin Sinawa suka mai da hankali kan daukar hotuna kawai, amma yanzu sun fi dora muhimmanci kan karfafa ilminsu a fannin al'adu. Madam Peng, wadda ta zabi dakin adana kayayyakin tarihi na lardin Hubei, da na birnin Jingzhou da kuma ginin Huanghe na lardin Hubei, wanda a kan ambata a cikin kasidar zamanin da na kasar Sin don yin yawon shakatawa. A cewar ta,

"A wannan lokacin hutu na mako guda, na kai ziyara biranen Wuhan, da Jinzhou na lardin Hubei, lallai na ji dadi sosai. Abun da ya fi burge ni shi ne, a wannan yankin mai dogon tarihi, na saurari sautin na kayan kida irin na Chimes da aka kera a shekaru fiye da dubu 2, har zuwa yanzu ana iya jin irin hali na zamanin da. Ginin Huanghe yana da kyan gani, bayan an hau kan ginin, ana iya ganin kogin Yantse mai fadi, hakan yana sawa a iya tunanin wasu shahararun kasidun zamanin da."

Baya ga haka, wasu ayyuka da hanyoyin yawon shakatawa dake mai da hankali kan fahimtar al'adu da dai sauransu sun fi samun karbuwa daga wajen Sinawa da suka zabi yin yawon shakatawa a kasashen ketare a wannan lokacin hutu. Bisa kididdigar da aka yi, an ce kasashe guda 10 da suka fi samun karbuwa a lokacin hutu din nan, su ne Faransa, Italiya, Switzerland, Jamus, Rasha, Amurka, Turkiya, Austria, Hadaddiyar daular Larabawa da kuma Czech da dai sauransu. Madam Zhao Shuang, wata jami'ar kamfanin yawon shakatawa na Tuniu na kasar Sin ta bayyana cewa,

"Sakamakon tasirin da gasar cin kofin duniya ke kawowa, Sinawa da yawa sun zabi kasar Rasha don yin yawon shakatawa, sun fi sha'awar kasar kan wasu wurare, ciki har da Red Square, fadar Kremlin, tabkin Baikal, majami'ar Kazan da kuma babban titin Nevsky da dai sauransu. Ban da wannan kuma, Turkiya da Masar da wasu kasashen dake yankin gabas ta tsakiya, da na Afirka ma sun samu karbuwa sosai daga wajen Sinawa."

Bisa karuwar matsayin kashe kudi a kasashen ketare na Sinawa, Sinawa dake kashe kudi ta hanyar salula a kasashen ketare sun fi yawa bisa na da, a wannan lokacin hutu na bikin kasa. Bisa kididdigar da kamfanin Alipay ya bayar, an ce a lokacin hutu na bikin kasar Sin na bana, yawan kudin da aka biya ta hanyar salula a kasuwar Bicester Village ta kasar Burtaniya ya ninka sau 90 bisa na makamancin lokacin bara, yawan kudin ya ninka sau 70 a cibiyar Dotonbori na birnin Osaka na kasar Japan, da kuma ninki 55 a filin jiragen sama na Sydney na kasar Australia. Madam Zang Xiaocheng, wata jami'a ta kamfanin Alipay ta bayyana cewa, an bullo da sabon halin musamman wajen kashe kudi a kasashen ketare da Sinawa ke yi, a cewar ta,

"A fannin kashe kudi ta hanyar salula da Sinawa ke yi, akwai wani babban canji a fannin shekarun haihuwa, wato a da Sinawa da shekarunsu na haihuwa suka kasa da 40, sun fi sha'awar zaben wannan hanya, amma a bana Sinawa da shekarunsu na haihuwa suka kai kimanin 60, wadanda suka zabi hanyar biyan kudi ta hanyar salula sun karu da kashi 90 cikin dari."

Baya ga haka, kididdigar da kamfanin Alipay ya bayar ta nuna cewa, yankunan da Sinawa ke kashe kudi a kasashen ketare sun habaka daga Asiya zuwa Turai da Amurka, har ma a duk fadin duniya. Ban da wannan kuma, ba su mai da hankali kan sayen kayayyaki kawai ba, a maimakon haka sun fi sha'awar shiga zaman rayuwar mazauna wuraren.

Game da sabon halin musamman da aka bullo a lokacin hutu na bikin kasar Sin na bana, wani mai nazari na jami'ar People's University ta kasar Sin Bian Yongzu yana ganin cewa,

"Ana iya gano cewa, Sinawa na soma neman gamsuwa a fannin tunani, bayan sun cimma burinsu a fannonin abinci da tuffafi, lallai matsayinsu na zaman rayuwa ya karu. Ban da wannan kuma, an nuna cewa, Sinawa sun kara imaninsu a kan makomarsu a nan gaba, hakan ya sa suna iya kashe kudi domin neman gamsuwa a fannin tunani." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China