Mai magana da yawun hukumar kula da kudaden musaya na ketare ta kasar Sin, Madam Wang Chunying ta bayyana cewa, a watan Satumba, kasuwar kudaden musaya na ketare ta kasar Sin ta bunkasa yadda ya kamata, kuma an yi musayar kudade daidai bisa tsari.
Madam Wang ta ce, duk da cewa akwai abubuwan rashin sanin tabbas da dama a nan gaba, amma tattalin arzikin kasar Sin na da karfi wajen shawo kan hadari daga kasashen waje, al'amarin da zai ci gaba da aza tubali mai inganci ga bunkasuwar kasuwar kudaden musaya na ketare, kana kuma asusun ajiya na ketare na kasar Sin zai ci gaba da kasancewa da karfinsa. (Murtala Zhang)