in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai jagorancin shiri na yankin Taiwan na kasar Sin ya mayar da martani ga jawabin mataimakin shugaban kasar Amurka
2018-10-07 20:53:24 cri

Yau ranar 7 ga wata, jaridar China Times ta yankin Taiwan na kasar Sin ta gabatar da wani sharhi wanda mai jagorancin shiri na yankin Huang Zhixian ta rubuta mai taken "mayar da martani ga mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence".

Ga yadda sharhin yake bayyanawa:

Ina jin bakin ciki sosai domin mataimakin shugaban kasar Amurka ya zargi kasar Sin, wato abokiyar kasar Amurka ba tare da tushe ba kafin zaben majalisar dokokin kasar.

Babu shakka ba ka san hakikanin tarihi sosai ba, ko kuma ka kyale shi ne da gangan. Kasar Amurka ba ta rasa wasu abubuwa domin kasar Sin ba, kasar Sin ta nuna sahihanci ga kasar Amurka.

Bisa tarihi, yayin da kasar Sin da kasar Amurka suka yi hadin gwiwa, aka kawo zaman lafiya ga dan Adam, kana kasar Amurka ta fi samun moriya. Lokacin da wasu kasashe masu karfi suka kai hari ga kasar Sin, an raba yankunan kasar Sin. Ko da yake kasar Amurka tana da manyan yankuna, amma ba ta janye daga kwace wani yanki ba. Lokacin da kasar Birtaniya ta samu yankin haya a birnin Tianjin, ita ma kasar Amurka ta samu wani yankinta na haya. Ba ta yi amfani da shi ba, sai ta sayar da shi ga kasar Birtaniya.

Ka taba bayyanawa game da bayar da kudi a shekarar 1900, lokacin da sojojin hadin gwiwa na kasashe 8 suka shiga birnin Beijing, da kwace yankunan kasar Sin, sai suka tilastawa Sin ta bayar da kudi da dama gare su da kudin daular Qing bisa ma'aunin azurfa kilogram miliyan 22 da dubu 500, wanda shi ne adadin kudin shiga da kasar Sin ta samu a shekaru 5. Ko da yake, kasar Amurka ba ta tura sojoji ba, amma ta samu kudi kashi 7.32 cikin dari. An kawo babbar illa ga kasar Sin maras karfi, kana shi ne kudin da jama'ar kasar Sin fiye da miliyan 100 suka yi kokari don samun shi.

Kasar Amurka ta yi hange nesa, domin ta riga ta fadada yankunanta, sai tana bukatar moriyar tattalin arziki da cinikayya da kuma tasirin da ta kawowa duniya a fannin siyasa. Shugaban jami'ar Illinois James ya mika wasika ga tsohon shugaban kasar Amurka Theodore Roosevelt cewa, idan kasar Amurka ta iya jawo daliban kasar Sin zuwa kasar Amurka, sai kasar Amurka ta iya sarrafa kasar Sin ta wannan hanya mai dacewa, wato hanyar ilmi da tunani.

A shekarar 1905, Amurka ta taba fitar da wata dokar kyamar kasar Sin, lamarin da ya sa Sinawa suka ki yarda da sayen kayayyakin kasar ta Amurka, daga baya gwamnatin Amurka ta dauki wani matakin mayar da wasu kudade ga gwamnatin daular Qing ta kasar Sin a wancan lokaci domin kawar da fushin Sinawa, hakika gwamnatin Amurka ta mayar da wasu kudaden diyyar da gwamnatin daular Qing ta kasar Sin ta ba ta, a sa'i daya kuma, kasar Sin ta tura wasu dalibai zuwa kasar ta Amurka domin yin karatu a can, ta hanyar yin amfani da wadannan kudaden, a sanadin haka, Amurka ta kara habaka tasirinta a kasar Sin cikin dogon lokaci, hakan shi ma ya gyara kimar Amurka a idon Sinawan wadanda suka sake fara sayen kayayyakin da Amurka ta kera.

Yayin yakin duniya na biyu, kasar Sin ta taba fama da rikici mai tsanani, amma Amurka ba ta nuna goyon baya gare ta ba, har ta dinga samar da kayayyakin da kasar Japan take bukata domin kai hare-hare ga kasar Sin. Ya zuwa lokacin da Japan ta kai hari ga tashar ruwa ta Pearl ba zato ba tsammani, sai dai Amurka ta sanar da cewa, za ta yi yaki da Japan, duk da haka Amurka ba ta samar da taimako ga kasar Sin ko kadan ba, adadin sojoji da fararen hula na kasar Sin da suka rasa rayukansu a yakin duniya na biyu ya zarta miliyoyi da dama, har an kusa kifar da gwamnatin kasar Sin a wancan lokacin, amma sauran kasashen duniya ba su kula da masifar da Sinawan suke fuskanta ba.

A cikin yarjejeniyar Yalta da aka daddale a asirce, wasu kasashen duniya, ciki har da kasar Amurka sun bata babbar moriyar kasar Sin kamar yadda suke so, bisa hakikanin tarihi, tsibirin Diaoyu yana karkashin mulkin kasar Sin ne, amma bayan yakin duniya na biyu, Amurka ba ta mayar da tsibirin ga kasar Sin ba, har ta baiwa Japan tsibirin, dalilin da ya sa haka shi ne domin Japan ta gabatar da rahoton sakamakon gwaje-gwajen da sojojin kasar ta runduna ta 731 suka yi a jikin Sinawan dake yankin arewa maso gabashin kasar Sin ga Amurka.

A halin da ake ciki yanzu kasar Sin ta samu kwanciyar hankali bayan hare-haren da aka kai mata, da yakin basasar da aka yi, da kuma kuskuren da aka aikata a cikin shekaru da dama da suka gabata, kuma har yanzu ba ta samu dayantakar yankinta ba tukuna, ban da haka, kasar Sin ba ta samu ci gaba ba a fannoni daban daban, amma tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, al'ummun kasar Sin sama da miliyan 1400 sun samu wadata bisa karo na farko a tarihi, a sanadin haka, muna darajanta sakamakon da muka samu matuka.

Abin da kasar Sin ta dogara wajen samun wadata da kwanciyar hankali a zamanin yau shi ne basirar jama'ar Sin da himma da kwazo da suka nuna, a maimakon kai hare-hare da yin mulkin mallaka. Kasar Amurka ma ta ci gajiya sosai daga yadda kasar Sin ke himmatuwa don neman samun ci gaba. Alal misali, Sinawa sun sayi kashi 30 bisa dari na duk yawan wayoyin salula mai tambarin Iphone, wadanda farashin ko wanensu ya kai dala 300. Amma kasar Sin ta samu dala 10 kawai wajen harhadar wayar salulan, yayin da Amurka ta samu dala fiye da 200.

Ci gaban wayewar kan bil Adama na da hanyoyi daban daban. Game da dukkan al'ummu da kasashen da aka taba kai musu hari, don me kasar Sin ita kadai ta samu wata hanyar musamman ta neman wadata? Dole ne a aza harsashi mai inganci wajen neman demokuradiyya, ganin yadda kasashe da dama ke fama da tabarbarewa da yake-yake bisa dalilin wai neman samun demokuradiyya.

Ba shakka akwai babban gibi a tsakanin Sin da Amurka daga dukkan fannoni. Za mu rubanya kokarinmu domin kara jin dadin zaman jama'armu da yaduwar al'adunmu. Amma bai kamata a tantance ci gaban kasar Sin bisa ma'aunin da kasar Amurka ta tsara ba. Mun gane cewa, sakamakon fin karfin da kasar Amurka ke da niyyar nunawa duk duniya, ba ta son ganin wadatar kasar Sin. Yanzu Amurka na daukar matakai daga dukkan fannoni domin shan kan kasar Sin. Amma wannan ba abin basira ba ne. Saboda Allah ba ya son ganin mulkin danniya da zaluncin da wani ya yiwa wani daban, kamar yadda Amurka ke yi a yanzu. Ana da imanin cewa, hanyar da kasar Sin ke bi ta neman ci gaban kanta yayin da amfanawa saura za ta taimakawa duk bil Adama, yayin samun amincewar Allah.(Jamila Kande Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China