Bankin jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, wasu kudin da za a samu sakamakon rage yawan kudin ajiyar zai biya rancen kudi na matsakaicin lokaci da kudi Yuan biliyan 450 da wa'adinsa zai kare a ranar 15 ga Oktoba. Ban da wannan kuma, rage yawan kudin ajiyar zai kara samar da kudi Yuan kimanin biliyan 750.
Bankin ya kara da cewa, zai ci gaba da aiwatar da manufofin kudi yadda ya kamata, da daidaita tsarin kudi, da sa kaimi ga samun bunkasuwar rancen kudi da tattara kudi a zamantakewar al'umma yadda ya kamata, ta hakan za a samar da yanayin hada-hadar kudi mai dacewa don samun bunkasuwa mai ingance da yin kwaskwarima kan tsarin samar da kayayyaki. (Zainab)