Kabila ya bayyana cewa, za a gudanar da bincike kan wannan batu, tare da gudanar da ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a sakamakon gobarar.
A ranar 6 ga wata da safe, wata motar jigilar mai ta yi karo da wata babbar mota dake tsaya a gefen titi, wanda ya haddasa samun gobara a motar jigilar mai, inda gobarar ta yi ta bazuwa cikin sauri. Ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin ya karu zuwa 50 ko ma fiye.
An ce, bayan da hadarin ya faru, mai ya dinga malala, mutanen dake kewaye sun yi ta kwasar man. Daga baya, gobara ta kama motar jigilar mai bayan da ta fashe, gobarar ta bazu a motoci da gine-ginen dake kewayen ta.
Bayan faruwar hadarin, tawagar MDD mai aikin kiyaye zaman lafiya dake kasar Congo Kinshasa sun tura motocin likitanci domin kai dauki ga mutanen da suka ji rauni tare da kwashe su zuwa asibitin birnin Kinshasa. (Zainab)