in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar dokokin kasar Afirka ta Tsakiya ya mika ta'aziyya ga Sinawan da suka mutu a kasar
2018-10-07 16:17:44 cri
Shugaban majalisar dokokin kasar Afirka ta Tsakiya Abdoul Karim Meckassoua ya tafi zuwa ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Afirka ta Tsakiya a jiya 6 ga wata, inda ya mika ta'aziyya ga Sinawa 3 da suka mutu a birnin Sosso-Nakombo dake kudu maso yammacin kasar a ranar 4 ga wannan wata.

Meckassoua ya bayyana cewa, a madadin majalisar dokokin jama'ar kasar, ya yi tir da harin da aka kaiwa Sinawa, tare da mika ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a sakamakon harin, kana da jajantawa iyalansu.

Jakadan Sin dake kasar Afirka ta Tsakiya Chen Dong, ya nuna godiya ga Meckassoua da ya mika ta'aziyya ga Sinawan da suka mutu, ya bayyana cewa, ana sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka tare da yin hadin gwiwa a tsakaninsu a tarihi, kowane irin laifin da aka samu ba zai hana Sin da Afirka su kara inganta tsarin raya makoma iri daya ba.

Daga bisani majalisar dokokin jama'ar kasar Afirka ta Tsakiya ta bayar da sanarwa, inda ta kalubalanci gwamnatin kasar da ta dauki matakan kama masu kai harin da gurfana da su a gaban kotu cikin hanzari.

A ranar 4 ga wannan wata, wani jirgin ruwa dake daukar Sinawa 4 da wani matashin kasar Afirka ta Tsakiya ya gamu da hadari, hakan ya haddasa matashin Afirka ta Tsakiya ya bace. Sai Sinawan suka tafi ofishin 'yan sanda dake wurin don neman taimako, amma wasu dakaru sun kai hari gare su a kan hanyarsu, wanda ya haddasa mutuwar Sinawa 3, wani guda ya ji rauni mai tsanani. Ya zuwa yanzu. 'yan sandan kasar Afirka ta Tsakiya sun kama mutane 3 da ake zarginsu da aikata wannan laifi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China