in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala yakin neman zaben shugaban Kamaru wanda za'a jefa kuri'ar ranar Lahadin nan
2018-10-07 15:50:34 cri

Jam'iyyun siyasa a jamhuriyar Kamaru sun kawo karshen gangamin yakin neman zaben shugaban kasar wanda ake sa ran jefa kuri'ar a ranar Lahadin nan, in ji hukumar zaben kasar.

Jam'iyyar (CPDM), mai mulkin kasar, ta yi gangamin yakin neman zabenta na karshe a Yaounde, babban birnin kasar a jiya Asabar. Shugaban kasar Paul Biya, wanda ke yiwa jam'iyyar takara, bai halarci gangamin na karshe ba, amma magoya bayansa sun ce yana nan tare da su a cikin ruhi, kana sun bukaci dukkan masu jefa kuri'ar da su zabi shugaban.

Shugaba Paul Biya, jagoran jam'iyyar ta CPDM, yana neman karin wa'adin shugabancin kasar na shekaru 7 bayan shafe shekaru 36 a karagar mulkin kasar.

Joshua Osih na jam'iyyar Social Democratic Front, dan takarar babbar jam'iyyar adawar kasar, ya yi gangaminsa na karshe ne a jiya Asabar a Douala, babban birnin kasuwancin kasar.

Osih ya shedawa magoya bayansa cewa, "A tsawon lokacin da muka kwashe muna gangamin yakin neman zabe, mun sha gabatar da shirye shiyen na neman zaman lafiya, da kwanciyar hankali da karuwar arziki a kasar. Muna yin hakan ne saboda Kamaru. A ranar Lahadi za'a zabi sauyi a kasar. Za mu lashe zaben."

Yan takarar jam'iyyun siyasa a kasar sun yi ta kiraye kiraye ga magoya bayansu da su tabbatar da zaman lafiya don gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China