in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Bayani mai lamba 301" na Amurka ya saba da ka'idar WTO, in ji kungiyar South Center
2018-10-06 15:55:31 cri
Kwanan baya, kungiyar South Center mai hedkwata a birnin Geneva na kasar Switzerland, ta fidda wani rahoto dake cewa, "bayani mai lamba 301" na kasar Amurka, ya saba da ka'idar kungiyar kasuwanci ta duniya wato WTO, ya kuma kalubalanci tsarin cinikin dake tsakanin kasa da kasa, kana ya kawo illa ga tattalin arzikin duniya.

"Bayanin mai lamba 301" shi ne ya tanadi doka mai lamba 301, dake cikin "dokar ciniki ta shekarar 1974" ta kasar Amurka. Bisa wannan tanadin doka, an ce, kasar Amurka tana da ikon gudanar da bincike kan tsarin ciniki na sauran kasashen duniya, idan ta yi zaton cewa, tsarin ba ya kan adalci. Haka kuma, tana da ikon yin shawarwari da gwamnatocin kasashen da abun ya shafa, sa'an nan, shugaban kasar Amurka zai yanke shawara kan yadda za ta mai da martani kan wadannan kasashe, kamar kara harajin kwastan, ko hana shigar da kayayyaki, ko kuma dakatar da yarjejeniyoyi masu nasaba da hakan da dai sauransu.

Cikin rahoton da kungiyar South Center ta fidda, an ce, kasar Amurka ta gudanar da wannan bincike mai lamba 301 bisa tsari na kasarta, a maimakon yin amfani da tsari na WTO, kuma matakan da ta dauka sun kalubalanci tsarin cinikin dake tsakanin kasa da kasa kwarai da gaske.

Haka zalika, an ce, ainihin dalilin da ya sa kasar Amurka ta dauki wadannan matakai bisa"bayani mai lamba 301" shi ne, hana bunkasuwar harkokin masana'antu, da fasahohin zamani na kasar Sin, a maimakon rashin adalci a fannin ciniki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China