in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manufofin Al'umma Na Karawa Kasa Karfi
2018-10-04 22:00:41 cri

Alkaluma a hukumance, sun nuna cewa, daga ranar 1 ga watan Oktoba, ranar farko ta makon hutun murnar kafuwar sabuwar kasar Sin, an yi tafiye-tafiye a cikin kasar da yawansu ya kai miliyan 122. An yi kiyasin tafiye-tafiyen sun samar da kudin shigar da ya kai RMB yuan biliyan 103 ga bangaren yawon bude ido, adadin da ya karu da kaso 7 idan aka kwatanta da na bara. Wannan karin da aka samu ya dasa ayar tambaya ga ikirarin da masu tsokaci ke yi na cewa kasar Sin na fuskantar raguwar harkokin kashe kudi.

Hakika rashin tabbas da ake fuskanta a duniya yanzu, ya sa tattalin arzikin kasar Sin ba ya tafiya yadda ya kamata kamar a baya. Gwamnatin kasar Sin ba ta musunta cewa akwai matsaloli ba, sai dai ta jadadda cewa, duk da kalubalen da ake fuskanta, kasar na ci gaba da bunkasa. Kuma alkaluman yawon bude ido na ranar farko ta murnar kafuwar sabuwar kasar Sin, sun nuna yakinin da Sinawa ke da shi kan makomar rayuwarsu da ma ta kasarsu.

A 'yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin ta sha fama da matsanantan kalubaloli. Wasu mutane daga kasashen yammacin duniya sun yi hasashen cewa kasar Sin za ta gamu da koma baya. Saboda yadda ta mayar da hankali kan al'amurran ketare na tattalin arziki, amma ba su lura da yadda Sinawa suka mayar da hankali wajen amfani da basirar kirkirar abubuwa ba, da irin juriyarsu, da halayyarsu ta hadin kai, da irin zumudin da suke da shi wajen tabbatar da ganin manyan mafarkin da suke da shi sun zama gaskiya.

Shugabanin Sin sun yi amana cewa mutanen da suke da wasu manufofi na gina kasarsu. Kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashen duniya 4 mafiya wayewa a duniya, da basirar kirkire kirkire, da hadin kai, da kwarin gwiwar yin aiki tukuru, a halin yanzu lamarin ya tabbata kamar yadda yake a baya. Wadannan halayen za su iya taimakawa kasar Sin wajen kawo karshen wahalhalun da suke fuskanta, da magance kalubaloli dake damunsu, da gina kyakyyawar makoma. Wadannan manufofin sun nuna irin taimakon da wadannan mutanen suka yi daga bangaren ilmin taurari da kuma kasancewa masu ginawa mutane abin da babu su a da wanda ya shafi fannonin masana'antu, makarantu, asibitoci, da baburan aika sakonni, kamar yadda suka tsaya tsayin daka wajen gina kyakkyawar rayuwa ga kansu da jama'ar kasarsu.

A halin da ake ciki, al'ummar Sinawa na zaune cikin yanayi na kwanciyar hankali, amma duk da haka a baya kasar Sin ta fuskanci kalubale mai zurfi, daga tashe tashen hankula na cikin gida da na waje. Wadannan lokuta masu wahala sun sanya kasar kara karfi. Sama da shekaru 100 da suka gabata, Sin ta fuskanci tursasawa daga 'yan mulkin mallaka. A halin yanzu kuwa, ya zama dole ta fuskanci kalubalolin ci gaba da ake samu a fannin bin ra'ayin gudanar da harkoki tare, da na harkokin kasashen waje.

Amma gamsuwa da irin nasarori da Sin ta samu, ba zai dakile ci gaban kasar ba. Wannan ne ya sa a shekarun baya bayan nan kasar ta samu tagomashi, daga shirin ta na farfado da tsohuwar hanyar Siliki, ta kuma kafa sabuwar mahada da za ta hade kasashe duniya daban daban, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.

Wasu mutane na yammacin duniya sun gaza fahimtar Sin, wasu kuma sun yi kuskuren fahimtar kasar, suna masu hasashen cewa Sinawa ba su da yakini ko manufofi. Amma fa hakan kuskure ne. Sinawa sun gamsu cewa, zaman jituwa ya fi tashin hankali, kuma zaman jituwa ya fi samar da alfanu ga kowa, Kana ka'idar nan ta "Ka yiwa saura kamar yadda kake son su yi maka." Ta hanyar bin ta, Sinawa na ci gaba da gina karfin kasar su. Kana suna aiki tukuru wajen tabbatar da cewa, Sin na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya da daidaito, tana kuma bunkasa ci gaba, a wannan duniya mai cike da rashin tabbas. (Masu Fassarawa: Fa'iza Mustapha, Ahmad Fagam, Saminu Hassan, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China