in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kirkire-Kirkire Shi Ne Babban Karfin Ci Gaban Kasar Sin
2018-10-03 21:26:52 cri
A duk lokacin da shugabannin kasar Sin na magana game da kirkire-kirkire, su kan tabo karin maganar da Sinawa da ke cewa, "idan har mutum ba zai motsa a rana ba, ya kamata ya kara kokari a kowace rana, har sai ya kai ga gaci."

Yau kusan shekaru dubbai, kasar Sin ta yi suna a fannin kirkire-kirkire, lamarin da ya kasance abin koyi kana abin da ya karfafawa al'ummarta gwiwar neman sabuwar hanyar bunkasuwa da ci gaba.

Tun bayan fara aiwatar da manufar gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje shekaru 40 da suka gabata, ake ta samun bunkasar ayyukan kirkire-kirkire a kasar. A shekarun baya-bayan nan, karkashin ingantuwar kirkire-kirkiren, an samu jerin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha, ciki har da kwangirin karbar sakonni da ake kira FAST wanda ke Guizhou; da tauraron dan Adam na "Wukong" mai nazarin wasu abubuwa masu sarkakiya da ake kokarin ganowa, wanda ya samo sunansa daga tsohon jarumin kasar Sin da ake kira Monkey King, da kuma tauraron dan Adam na "Micius" mai hidimar sadarwa kuma mai aiki da sinadarin "quantum" da tsaron intanet na farko a duniya, wanda ya samo sunansa daga masanin falsafa da kimiyya na karni na 5 dan kasar Sin.

A aikace, kasar ta dogara ne kan kirkire-kirkire mai zaman kansa a kokarin samun sabbin sauye sauye a fannin kimiyya da fasaha wanda hakan zai taimakawa ci gaban tattalin arzikin kasar. Karfin tattalin arzikin kasar zai iya haifar da samun kudaden da za'a yi amfani da su wajen ayyukan kimiyya da fasaha. Gwamnatin kasar, kamfanoni, da cibiyoyin kasar sun hada hannu wajen tabbatar da ganin ci gaban kimiyayya da fasaha a fannin fasahar kirkire kirkire ya taimaka wajen ci gaban masana'antu tare da taimakawa wajen inganta yanayin zaman rayuwar alumma.

(Ibrahim Yaya, Faeza Mustapha, Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China