in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta horas da 'yan sanda yadda za'a dakile barazanar ta'addanci a Somaliya
2018-10-02 15:21:37 cri
Shirin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a kasar Somaliya (AMISOM), ya sanar a jiya Litinin cewa, ya horas da jami'an 'yan sanda 100 dabarun dakile barazanar hare haren ta'addanci a shingayen binciken ababen hawa na jami'an tsaro a kasar Somaliya.

Hukumar ta AU ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar a Mogadishu cewa, makasudin gudanar da kwarya-kwaryar bada horon shi ne, don lalibo hanyoyin da za'a gudanar da binciken ababen hawa ta hanyar amfani da matakan dakile hare haren ta'addanci.

Christine Alalo, mai rikon mukamin kwamishinan 'yan sandan AMISOM ya fada cikin wata sanarwa cewa, wannan shirin bada horo ya zo ne a daidai lokacin da ake burin tabbatar da kawo sauye sauye ga 'yan sandan AMISOM da kuma taimakawa 'yan sandan Somaliya don su samu kwarewa.

Jami'an da suka samu horon za su koyar da takwarorinsu na Somaliya irin kwarewar da suka samu a yayin shirin.

Alalo ya bukaci jami'an 'yan sandan na AMISOM da su yi amfani da ilmin da suka samu wajen inganta al'amurran tsaro a Mogadishu da sauran biranen kasar.

Shirin dai wani bangare ne na ci gaba da gina tsarin tabbatar da tsaro, domin baiwa jami'an damar dakile hare haren da ake kaiwa ta hanyar amfani da abubuwan fashewa, wadda ita ce kadai hanyar da mayakan al-Shabab ke amfani da ita a halin yanzu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China