in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bukukuwa a kasar Sin don murnar cika shekaru 69 da kafuwar kasar
2018-10-01 21:20:35 cri

A yau wato ranar 1 ga watan Oktoba, an samu cika shekaru 69 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. A wannan rana ta musamman, jama'ar kasar dake wurare daban daban sun shirya bukukuwa domin taya juna murnar ranar. Wakilinmu Ahmad Fagam na dauke da karin bayani dangane da wannan muhimmin biki.

Da misalin karfe 6 da 'yan mintuna na safe, wasu sojoji masu kare tutar kasar Sin da suke wakiltar rundunar sojojin teku, da kasa, da sama na kasar Sin sun kai tutar kasar mai launin ja da kuma rawayen taurari guda 5 a kanta zuwa filin Tian'an'men dake tsakiyar birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin.

Yayin da ake taken kasar Sin, an daga tutar kasar sannu a hankali zuwa kololuwar sandar. A sa'i daya kuma, an samu jama'a da yawa da suka taru a wajen filin Tian'an'men don ganewa idanunsu yadda aka gudanar da wannan mihimmain biki.

"Na zo nan da karfe 9 na daren jiya. Hakika ina cike da kaunar kasarmu har ba zan iya bayyana wannan kauna da kalmomi ba. Ina alfahari sosai ganin yadda na samu damar tsayawa a nan a yau."

"Na yi zumudi matuka yayin da aka daga tutar kasar, a nan ina so in taya murnar kafuwar sabuwar kasarmu!"

"Ina alfahari da kasarmu, da fatan za ta samu cika burinta na samun babban ci gaban zaman al'ummarta cikin hanzari."

A yau Litinin, an kaddamar da bikin yawon shakatawa na kasa da kasa na birnin Beijing karo na 20, wanda aka yi masa taken "Kaunar da aka samu tsakanin Sin da Afirka, da haduwa a birnin Beijing". Inda aka samu kungiyoyin masu fasahar al'adu na kasar Sin da na kasashen waje guda 30 da suka taru a cikin wani wuri mai ni'ima mai taken "Beijing Olympic Park", don nunawa masu kallo fasahohin al'adu da samar da wani yanayi na annashuwa. Ashraf Taha, shi ne shugaban kungiyar masu fasahar al'adu ta kasar Masar, wanda ya bayyana cewa,

"Kasar Sin da kasar Masar suna hadin gwiwa da juna a fannin musayar al'adunsu tare da samar da dimbin sakamako. Yau rana ce da aka kebe domin tunawa da kafuwar kasar Sin. Muna godiya ga gwamnatin kasar Sin kan yadda ta gayyace mu domin mu nuna fasahohin al'adunmu a wannan rana ta musamman. Ta wannan hanya za a iya karfafa zumunci tsakanin kasashenmu, tare da ba da kyakkyawar damar cudanyar al'adu."

A yayin da ake murnar bikin tunawa da ranar kafuwar sabuwar kasar Sin, an kayatar da biranen kasar don samar da wani yanayi mai kyan gani. A birnin Shi'jia'zhuang na lardin Hebei, an ajiye furannin iri-iri a dab da tituna, wadanda ke da launuka daban daban. Wurare masu ni'ima na birnin su ma sun zama tamkar teku na furanni. Ta wannan hanya, jama'ar birnin suna nuna murnarsu kan wannan biki mai muhimmanci. Zhang Yiliang, shi ne jami'i na hukumar kula da aikin dasa bishiyoyi na birnin Shi'jia'zhang, wanda ya ce, don samar da wani muhalli mai kyau ga jama'ar birnin, an tsara wasu wuraren ajiyar dimbin furanni 28, cikin wasu wuraren yawon shakatawa 17, bisa ainihin abun da ake nunawa a wadannan wuraren.

"A wannan lokacin da ake murnar bikin tunawa da kafuwar kasa, mun nuna wasu furanni da yawansu ya kai miliyan 1.07, tare da wasu manyan bishiyoyi. Da wannan da kuma sauran wasu furannin iri 2 da ake samun musamman ma a wannan lokaci, mun tsara wasu wuraren nuna furanni masu ban sha'awa."

A tituna da unguwanni na birane daban daban na kasar Sin, an samu saukin gano tutocin kasar Sin, mazauna suna ta yin shirin murnar wannan muhimmiyar rana.

"Muna fatan kasarmu ta kara samun bunkasuwa da karfi da kuma wadata, sannan jama'a fararen hula su ji dadin zamansu cikin koshin lafiya."

A wasu biranen kasar Sin, ciki har da Beijing, Shenzhen, Hangzhou, Harbin da kuma Xiamen, an yi amfani da hasken fitilu wajen bayyana kalmomin "Ina Sonki, Kasar Sin" a kan gine-gine domin kawatar da daren a biranen.

A yankunan karkarar kasar Sin, ranar murnar kafuwar sabuwar kasar, lokaci ne na murnar girbin hatsi. A wata gasar wasannin motsa jiki ta manoma da aka shirya a wani garin dake lardin Jiangxi, manoma suna farin ciki suna wasa domin murnar girbin da suka samu.

"Duk jikina ya jiku, amma ina farin ciki sosai."

An riga an shirya wannan gasa a garin Yinhe na gundumar Luxi ta lardin Jiangxi har sau 4, inda take jawo manoma 'yan wasa fiye da 1000 da su halarci wannan gasa. Mr. Zhong Liangzan, jagoran garin Yinhe na gundumar Luxi ya gaya wa wakilinmu cewa, "Muna fatan karin mutane za su ga ci gaban da garinmu Yinhe ya samu wajen zamanantar da aikin gona, su kuma ji dadin wasa a kauyuka, kuma su san irin farin ciki da manoma suke yi sakamakon girbin hatsi da suka samu." (Sanusi Chen, Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China