in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da bikin daga tutar Sin a filin taro na Tian'anmen domin murnar ranar kafuwar sabuwar kasar Sin
2018-10-01 15:45:47 cri

Da sanyin safiyar yau Litinin ne aka gudanar da bikin daga tutar kasar Sin, a filin taro na Tian'anmen dake nan birnin Beijing, a wani bangare na bikin murnar cika shekaru 69 da kafuwar sabuwar kasar Sin.

Rukunin dakarun sojin 'yantar da al'umma na kasar Sin ko PLA a takaice, sun raka tutar zuwa filin taron, yayin da sojojin badujala ke kada taken kasar.

Kimanin 'yan kasar ta Sin 145,000 daga sassa daban daban ne suka halarci dandalin na Tian'anmen, domin ganewa idanunsu yadda bikin zai gudana.

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1949 ne aka daga tutar kasar Sin a karon farko a filin na Tian'anmen, lamarin dake nuni ga kafuwar sabuwar kasar Sin ta zamani ga al'ummar Sinawa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China