Mr. Li Keqiang ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, yayin da ya halarci bikin karrama wasu baki 'yan kasashen waje, da suka samu lambobin yabo na sada zumunta na Sin, wanda ake bayarwa a duk shekara, ga wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da kasar ta Sin gaba.
An dai gudanar da bikin ba da lambobin yabon ne a dakin taruwar jama'a dake nan birnin Beijing,
Firaministan ya ce irin wadannan kwararru 'yan kasashen waje, na ba da gudummawar gaske, a fannin raya tattalin arziki da zamantakewa, da musaya tsakanin Sin da kasashen waje.
Mr. Li ya kara da cewa, Sin na maraba da karin gudummawar baki 'yan kasashen ketare, a fannin samar da ci gaban kirkire kirkire. Yana mai fatan za a hade basirun gida da na kasashen waje wuri guda, domin bunkasa kirkire kirkire, da fadada ci gaban ilimin kimiyya na duniya, da kara wayewa a fannin raya fasahohi da ci gaba, da kuma samar da ci gaba cikin lumana, da hade sassan ci gaban duniya wuri guda. (Saminu Hassan)