Mai magana da yawun hukumar kula da bala'u ta kasar Sutopo Purwo Nugroho shi ne ya sanar da hakan, yana mai cewa, girgizar kasa ba kakkautawa masu karfin maki 6.0 da 7.4 gami da tsunami mai karfin maki 6.1 ne suka yi kaca-kaca da lardin. Sai dai bala'in ya fi shafar wani yanki a Palu, babban birnin lardin da kuma gundumar Donggala.
Kakakin ma'aikatar watsa labarai da sadarwa na kasar Ferdinandus Setu ya ce, a jiya Asabar babban filin jirgin saman lardin yana gudanar da ayyukan jin kai ne kawai. Haka kuma na'urorin sadarwa a sassan daban-daban na lardin suna aiki yadda ya kamata. (Ibrahim)