A karshen makon nan ne 'yan sanda da suka fito daga kasashen Kenya da Zambia da Uganda da Saliyo, za su bar kasar dake kahon Afrika, bayan shafe shekara 1 suna aiki karkashin shirin na AMISOM.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, mukaddashiyar Kwamishinan 'yan sandan AMISOM Chritine Alalo, ta jadadda muhimmiyar rawar da 'yan sandan suka taka, wajen karawa rundunar 'yan sandan Somalia karfi, dake iya aiwatar da ayyukan tsaron al'umma bisa kwarewa.
An ba jami'an wadanda suka gudanar da ayyuka na musammam, lambar yabo a Mogadishu, saboda namijin kokarin da suka yi da gudunmuwar da suka bayar ga wanzuwar zaman lafiya a Somalia. (Fa'iza Mustapha)