in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayar da takardun da aka cimma a taron kolin Beijing na FOCAC a matsayin takardun babban taron MDD
2018-09-29 16:40:02 cri
Jiya Juma'a, sashen sakatarorin MDD ya bayar da sanarwar Beijing game da karfafa kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka, da shirin aikatawa na Beijing na FOCAC tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021, wadanda aka zartas a gun taron koli na FOCAC da aka shirya a Beijing, an bayar da takardun biyu ne a matsayin takardun hukunce ne na babban taron MDD. Wannan ne kuma karo na farko da babban taron ya bayar da takardun da aka cimma a FOCAC.

An zartas da takardun biyu ne a gun taron koli na FOCAC da aka shirya a ranar 4 ga watan Satumban shekarar 2018 a birnin Beijing, sun kuma kasance jagora wajen yadda za a bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a wasu lokuta masu zuwa.

Bayar da takardun biyu a MDD zai karfafa tasirin taron kolin, da taimaka wa kasashe daban daban wajen kara fahimta da nuna goyon baya kan hadin kai tsakanin Sin da Afrika. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China