in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaddamar cinikayya za ta cutar da Amurka, in ji wani masanin tattalin arziki
2018-09-29 16:30:20 cri
Shugaban wata cibiyar horaswa game da harkokin cinikayya, da tsare tsare, da harkokin kasa da kasa dake Amurka William Reinsch, ya ce takaddamar cinikayya tsakanin Sin da Amurka za ta yiwa tattalin arzikin Amurkar illa, ta fannin gurgunta tsarin cin gajiya daga haraji, da hauhawar farashin hajoji ga masu sayayya.

Mr. William Reinsch, ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Ya ce a yanzu haka Amurka na cin gajiya daga raguwar haraji, wanda ta fara samu tun daga karshen shekarar bara. Sai dai kuma saurin ci gabanta zai ci karo da raguwar hada hadar cinikayya, da hauhawar farashi ga masu sayayya, matakin da zai sauya yanayin saurin bunkasar tattalin arzikin kasar.

Da ya tabo batu game da tasirin hakan ga tattalin arzikin duniya kuwa, Mr. Reinsch ya ce takaddamar cinikayya, za ta rage saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, wanda hakan zai shafi tsarin ba da kariyar cinikayya.

Ya ce idan wata kasa guda ta cimma nasarar karya dokokin cinikayya, musamman ma babbar kasa, hakan zai sanya sauran kasashe su samu karfin gwiwar yin hakan ba tare da wani shayi ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China